Birtaniya Ta Yi Allah Wadai Da Harin Makami Mai Linzami Da Iran Ta Ce Ta Yi Wa ‘Yan Ta’adan Amurka

  • Home
  • Labarai
  • Birtaniya Ta Yi Allah Wadai Da Harin Makami Mai Linzami Da Iran Ta Ce Ta Yi Wa ‘Yan Ta’adan Amurka

A ranar Laraba nan Birtaniya ta yi Allah wadai da harin makami mai linzami da aka kai Iraqi kan sansanin sojojin hadaka.
Za a iya tunawa gidan talabijin na Iran ya bayyana cewa ‘yan tadda 80 na Amurka sun halaka tare da lalata jiragen saukar ungulu da wasu kayan yaki.
“mun yi Allah wadai da wannan hari kan sansanin sojoji a Iragi da ke dauke da sojojin hadaka, wanda ya kunshi dakarun Birtaniya,” Inji sakataren harkokin waje, Dominic Raab.
Sakataren ya nuna damuwarsa kan rahoto da suka samu na barnar da aka yi ta amfani da makamai masu linzami, wanda suka yi awon gaba da manyan jiragen sama biyu dake dauke da dakarun Amurka sama da ashirin da biyu, da dakarun Iran suka harbo.
Sashen tsaro na Amurka ya bayyana cewa makaman masu linzami sun sauka a bangare biyu da suka hada da Irbil da Al Asad.
Gwamnatin Iran ta sha alwashin daukar fansa kan kisan da aka yi wa babban habsan sojanta, kuma kwamandan sojan kasar Qasem Soleimani a ranar juma’a, ta hanyar amfani da jirgi mara matuki da sojojin Amurka suka yi.

%d bloggers like this: