DANDALIN MARUBUTA A SHEKARA TA 2020

  • Home
  • Adabi
  • DANDALIN MARUBUTA A SHEKARA TA 2020

A ranar Lahadi ne 5 ga watan Janairu, 2020 aka gudanar da Dandalin Marubuta na Kungiyar ANA Kano, wanda ya kasance na farko a cikin shekara ta 2020. Dandalin ya kunshi zallar marubutan Hausa, kuma ana gudanar da shi ne a duk Lahadin farkon wata a dakin karatu na Murtala Muhammad dake Kano, inda shadkwatar kungiyar ta ke.


Taron ya samu halarta manya da kananan marubuta da suke rubutu cikin harshen Hausa, wanda suka hada da shugaban kungiyar ANA Kano, Zaharaddeen Ibrahim Kallah da shugaban Kungiyar mawaka ta kasa reshen jihar Kano, Ibrahim Hamisu da Kabiru Yusuf Anka tare da Sadisu Usman. Sauran sun hada da Abdullahi Lawan Kangala da Abba Shehu Musa, da Hassan Ibrahim Gama, da Almujtafa Habibullah sai Zaidu Barmo da sauransu.


An fara taron ne bayan shugaban marubuta ya yi jawabin maraba tare da waiwaye ga abubuwan da suka faru ga marubuta a shekarar da ta gabata. A cewarsa marubuta da dama sun samu yin aure wanda suka kunshi maza da mata a Kano da makwabtan jihohi, musamman a Katsina. Ya yi addu’ar Allah ya albarkaci auren, sannan wadanda abin bakin ciki ya faru da su Allah ya yaye musu tare da maida musu da alheri. Shugaban ya yi bayani marubuta sun gudanar da tarurruka a shekarar da ta gabata a kungiyance tare da hadaka da wasu hukomomi da suka hada da Dakin Karatu na Murtala Muhammad da Hukumar Kare Hakkin Mallaka da Babban Dakin Kararu na Kasa, sai kuma sashen Amurka dake Kanon da sauransu.


Shugaban ya baiyana kudirin kungiyar na sauya tafiyar ANA Kano, inda za a yi mata garanbawul a shekarar da ake ciki. A cewarsa. “Shugabancin kungiya ya kafa kwamiti da aka ba wa alhakin zama da yin tunani na yadda za a kirkiro da sababbin shirye-shirye da za su ciyar da adabi gaba.” A jawabinsa ya kara da cewa. “Muna sa ran marubuta za su tafi da zamani, musamman yadda harkar rubutu ta koma kafar yanar gizo, wanda kasuwancin littafi da yada shi ya ta’allaka da wannan kafa.”
Shugaban ya yi jaddada kudirin kungiyar na bada horon sanin makamar aiki ga marubuta, musamman ta sabon salon rubutu na zamani.


An gabatar da rubuce-rubuce na wakoki tare da rubutun zube na gajeren labari a yayin taron. Daga cikin rubutun da aka gabatar akwai waka mai taken “Tauraruwa” da Abdullahi Lawan Kangala ya gabatar, wacce ya alakanta ta ga tashar radiyo ta Arewa. Sai kuma waka mai suna “Hauwa Kulu” da Adamu Yusuf Indabo ya gabatar, wacce ke nuna bege ga Hauwa Kulu tare da siffanta kyan ta. Ibrahim Hamisu ya gabatar da waka mai suna “Makaryaciya” inda ya yi gugar zana ga wata da ya kira makaryaciya saboda dabi’unta marasa kyau.


Kabir Yusuf Anka ya gabatar da gajeren labari mai taken “Buhari Ya Zaga” wanda rubutu ya yi duba ga wani matashi da ya yi wa abokinsa ta’annati da almakashi, a zuwan ya zagi Buhari, wanda ya shiga komar ‘yansanda. Rubutu na gaba da ja hankali waka ce mai taken “Ilimi Haske” da Almujtafa Habibullah ya gabatar dake karfafa amfanin ilimi ga dan adam. Rubutun ya kawo tattaunawa a kan amfani ilimi, wanda ya zarta amfanin kudi ga rayuwar dan adam.
Zan rufe da wakar Hauwa Kulu domin jin dadinku.

Hauwa Kulu
By
Adamu Yusuf Indabo

Ya Allahu za na rubuta,
Waka wacce zan rera ta.

A kan gimbiyar ‘yan mata,
Hauwa Kulu zan yi yabon ta.

Na wassafa kyan surarta,
Hauwa Kulu manyan mata.

Fuskar taki ta kasaita,
Mai hanci abun a kwatanta.

Idanunki giwar mata,
Ababan yabo da nagarta.

Da bakinki fes mai tsafta,
Haba taki ta gigita.

Samarin da sun ka dimauta,
Da kyawunki hasken mata.

Wuyan ma abun a misalta,
Don samun sa za ya wahalta.

Kamar sa a jimlar mata,
Hauwa Kulu kin gawurta.

Da kirjinki mai kyan fata,
Fatar taki ta bambanta.

Sannan cibiyar kyawunta,
Ta zarce Adamsy ya furta.

Hauwa Kulu giwar mata,
Gwana santalar cinyarta.

Mai santsi da laushin fata,
Hauwa Kulu duk siffarta.

Da kyawun gani surarta,
Domin ta wuce kushe ta.

Haka lafazin muryarta,
Da zaki idan ta furta.

Kamar wacce an tace ta,
Sarewa da an busa ta.

Muryar Hauwa ta zarta ta,
Ashe Hauwa ta ciri tuta.

Tutar kyau da tutar tsafta,
Fara doguwa da nagarta.

A nan gun fa za na takaita,
To ya kun ji kyan surarta?

Hauwan nan da babu kazanta,
Ra’ayinku za na rubuta.

A wakar kashi na Biyunta,
Wakar Hauwa giwar mata.

A yau Laraba na rubuta,
Ta farkon da kun gama jin ta.

Na ce bay ga duk maji;yanta,
Sai kun ji ni in na huta.

%d bloggers like this: