Dangote ya shiga sahun masu kudin duniya 100

  • Home
  • Labarai
  • Dangote ya shiga sahun masu kudin duniya 100

Mai kudin Afirkan nan kuma haifaffen Kano, Alhaji Aliko Dangote ya shiga sahun mutane 100 da suka fi kowa arziki a duniya.


Kafar Bloomberg ce ta fitar da wannan labari wanda ya nuna Aliko Dangote na a matsayi na 96 a duniya tare da zunzurutun kudi har dalar Amuraka biliyan 4.3 a karshen shekara da aka yi bankwana da ita, wanda ke samun kudaden shiga daga siminti da filawa tare da sukari.


Aliko Dangote mai shekara 62 ya kare shekarar bara ta 2019 da dalar Amurka biliyan 15 a cikin lalitarsa, wanda hakan ya tabbatar da shi a matsayi na 96 a jerin hamshakan masu arziki na duniya.


Kafar ta ruwaito cewa tauraruwar Dangoten ta haskane saboda nasibin da ya samu a harkar kasuwancin siminti inda yake rike da kashi 85% na ainahin jarin wannan masana’anta.


Dangote na rike da manyan hannun jari a wasu masana’antu da suka hada da Dangote Sugar da Nascon Allied Industries da Dangote Flour Mills sai kuma bankin United Bank for Africa.
Dukkan hannun jarinsa ana juya su ne a karkashin masana’antar Dangote Industries, wacce ke da hannu a kasuwancin abubuwa sha da takin zamani tare da harkar mai.


Masana’antarsa ta sarrafa takin zamani na da karfin jari da yake iya sarrafa takin zamani har na tan miliyan 2.8 a shekara.


Aliko Dangote ya zuba jarin dalar Amurka biliyan 12 a cikin harkar samar da katafariyar matatar mai a Najeriya, wanda ba ta cikin lissafin adadin kudadensa kasancewar ba ta fara aiki ba.


Hamshakin mai arzikin ya mallaki manyan gidaje na zama da haya guda shida a birnin Ikko, wanda aka yi musu kiyasi ta kudin haya da suke samarwa, a ta bakin mai magana da yawun Dangoten Anthony Chiejina.

%d bloggers like this: