An Kai Mummunan Farmaki A Wasu Garuruwan Jihar Katsina

  • Home
  • Labarai
  • An Kai Mummunan Farmaki A Wasu Garuruwan Jihar Katsina

An Kai Mummunan Farmaki A Wasu Garuruwan Jihar Katsina

Daga Yaseer Kallah

Wasu ‘yan bindiga, a daren Asabar, sun kai farmaki wasu garuruwa guda 4 na karamar hukumar Dutsin-ma, jihar Katsina, inda suka dauke mutane 3, tare da sace dabbobi 100.

‘Yan bindigar sun dauke mutane biyu, Sale Rama da Bilkidu Sunusi a kauyen Maitsani, yayin da suka dauke wani mutum mai suna Alhaji Bello Sule a kauyen Darawa.

Sun kuma sace akalla shanu 60 da tumaki 40 a kauyen Madagu, inda kuma suka sace dabbobi masu yawa a kauyen Gefen Kubewa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka cikin kauyukan a cikin dare inda suka shafe kimanin awanni hudu suna ta’annatin. Sun kuma bayyana cewa a cikin satin da ya gabata, da wuya rana ta zo ta wuce ba a kai farmakin da zai salwantar da rayukan wasu ko kuma a yi garkuwa da wani.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da afkuwar abin inda ya ce tuni an kai jami’an tsaro gurin domin kawo karshen tashin hankalin.

%d bloggers like this: