Sarkin Kano ya amshi shugabancin majalisar sarakuna

  • Home
  • Labarai
  • Sarkin Kano ya amshi shugabancin majalisar sarakuna

A cikin awa ashirin da hudu da rubuta takarda daga gwamnatin Kano tana son mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya bada amsa ko ya karbi tayin gwamnati na zama shugaban majalisar sarakuna ta Kano ko akasin haka, sarkin ya amsa wannan tayi na gwamnati.

Za a iya tunawa a watan 9 ga watan Disamba, 2019 mai girma gwamna ya ayyana sarkin a matsayin shugaban majalisar sarakunan. Amma tun daga wannan lokaci ba a ji ta bakin sarki ko amsarsa kan wannan tayi.

A yanzu ne ta hannu sakataren masarautar Kano mai rikon kwarya ya bada sanarwa Sarki ya karbi wannan mukami, inda ya ce ai Sarki ba ya ki karbar mukamin ba.

Sai da sarkin na sauranon wasu bayanai daga gwamnan Kano, musamman dangane da tabbatar ayyukan sauran mambobin kwamitin, samar da mahalli na sakatarori da duk abubuwan da suka shafi gudanarwa.

%d bloggers like this: