Majalisa ta amince da kasafin kudin shekara 2020

  • Home
  • Labarai
  • Majalisa ta amince da kasafin kudin shekara 2020

Majalisar dattawa ta amince da kasafin kudin shekara ta 2020, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a gabanta. Sai dai majalisar ta kara adadin kudin daga zambar kudi tiriliyan 10,330,416,407,347 zuwa zambar kudi tiriliya 10, 594.362,364,830.
Haka nan majalisar dattawan ta kara adadin kudin da aka kaiyade na hasashen farashin danyen mai daga $55 zuwa $57. Sai dai ta bar adadin yawan danyen man da za a dinga fitarwa akan miliyan 2.18 a duk gangar mai.

%d bloggers like this: