Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gargadi Gwamna Ganduje

  • Home
  • Labarai
  • Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gargadi Gwamna Ganduje

Fitatcen malami kuma daya daga cikin shugabanni na darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje akan yunkurinsa na kara kirkirar masarautu a Kano. A cewarsa magoya bayan darikar ta Tijjaniyya ba sa goyon bayan wannan yunkuri na shi.
Malamin ya fitar da wannan bayani ne ta sakon muryarsa da aka turo wa jaridar AMON NASARA.
A sakon ya ce: “Ina rokon Ganduje don Allah, don Annabi ya bar batun kirkiro da sababbin masarautu, kamar yadda kotu ta soke su.”
“Ina jan hankalinsa ya janye maganar nan, yadda kotu ta rushe wadannan abubuwa nasa, to ya hakura tun da kotu ta mayar da Kano kamar yadda take shekara dubu da wani abu.”
Ya kara da cewa, “Ganduje ya kammala aikinsa cikin zaman lafiya, ya fi kan ya kammala ana tsine masa.”
Ya cigaba, “taba fadar Kano, taba mu ne gaba daya ‘yan Tijjaniya da masoyanmu.”
Shehun Malamin ya bada misali ga yadda turawan mulkin mallaka suka zo kasar, amma har suka gama mulkinsu ba su ruguza abin da suka zo suka tarar a Kanon ba shekara da shekaru. A saboda haka ne ya nemi Gwamnan ya janye wannan yunkuri. A cewar malamin suna tare da masarautar Kano, kuma ko ba su da karfi a zahiri suna da karfin addu’a.
Wannan jawabi ya biyo bayan aika wani sabon kudiri ga majalisar jihar da aka yi ranar Litinin domin kafa sababbin masarautun.
A ranar 21 ga watan Nuwamban wannan shekara ne babbar kotu a Kano karkashin mai shariah Usman Na’Abba ta bada hukunci rushe masarautun da aka kirkira a Kano, wanda gwamnan Kano ya rattabawa hannu a ranar 8 ga watan Mayu, 2019. Sababbin masarautun da aka kirkira a wannan lokacin sune Bichi da Karaye da Rano da Gaya.
 

%d bloggers like this: