‘Yan Mata Shida Sun Mutu A Cikin Ruwa Yayin Da Kwale-Kwale Ya Kife Da Su A Kebbi

  • Home
  • Labarai
  • ‘Yan Mata Shida Sun Mutu A Cikin Ruwa Yayin Da Kwale-Kwale Ya Kife Da Su A Kebbi

‘Yan Mata Shida Sun Mutu A Cikin Ruwa Yayin Da Kwale-Kwale Ya Kife Da Su A Kebbi

Wasu ‘yan mata guda shida sun halaka a cikin kogi yayin da kwale-kwalen da suke kai ya kife da su a kauyen Tindifai da ke Dakingari, karamar hukumar Suru, jihar Kebbi.

Daily Trust ta rawaito sunayen yaran da suka nutse kamar haka: Hadiza Garba (15), Lauratu Muhammad, (13), Adama Musa (15), Firdausi Garba (13), Maryam Abdullahi AbdulRahnan (13) da Suwaiba Abdullahi AbdulRahama (10).

Bayan nan matukin kwale-kwalen, Umar Faruk, dan shekara 13 ya samu nasarar kubutar mata uku.

Hadarin ya rutsa da yaran yayin da suke kokarin ketare wani kogi domin zuwa gonar shinkafa don gabatar da aikin girbi.

Da yake tabbatar da labarin afkuwar hadarin, babban sakataren yada labaran gwamnan Kebbi, Mu’azu Dakingari, ya bayyana cewa an samu nasarar samo gawarwakin yara biyar a cikin kogin, yayin da kuma ake kan kokarin samo gawar yarinya ta shidan.

A nashi jawabin, shugaban karamar hukumar Suru, Alhaji Umaru Maigandi, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya bar kauyen Tindifai dauke da mata guda tara domin zuwa wata Fadama da ke yankin, kafin ya kife.

Ya daura alhakin hadarin a kan cincirindon da aka yi a kan kwale-kwalen. “An gina kwale-kwalen domin daukar mutane biyar kacal,” ya fada.

Tuni aka yi wa ‘yan mata biyar din jana’iza tare da rufe su kamar yadda addini Musulunci ya koyar.

%d bloggers like this: