AN GANO FARFESOSHIN BOGI 100

A lokacin da kungiyar malaman jamia ta ASUU ke musayar yawu da gwabnatin tarayya akan tsarin biyan kudi na bai daya wato IPPIS, a daidai lokacin ne kuma aka bayyana bankado wasu farfesoshi guda 100 na bogi.


Babban Sakataren hukumar kula da manyan makarantu na jami’a (NUC) Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana haka a mujallar hukumar ta watan Nuwamba.


Ya kuma ce tuni hukumar ta buga sunayen farfesoshi na bogi a shafinta na yanar gizo, sannan ta aikawa da jami’oi sunayen don tantancewa.
A taron da ya yi da shugabannin makarantun jami’a ya bayyana cewa a watan Disamba na 2019 za su sabunta takardun bayanai, wanda dukkan farfesoshi da jami’oin da suke za su shiga su dora bayanansu a shafinsu. A cewarsa wannan zai taimaka wajen bankado farfesoshin na bogi.


“Wannan hanya ce ta gano farfesoshin bogin dake cikin tsarin. Yaki da jabun farfesoshi abu ne da ya shafi kowa da kowa.” A cewarsa.


Abubukar ya sanar da shugabannin makarantun na jami’a tare da Babban Darakta hukumar hidimar kasa (NYSC), Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim cewa akwai korafi akan yadda wasu daga masu hidimar kasa ba sa iya kare kwalin digiri da suka samu daga manyan jami’oin kasar nan.


Hakan yasa ya ummarci shugabannin jami’oin da su yi bincike akan manyan makarantu da suka kulla alakar ilimi, domin dole jami’oi su jagoranci yaki da rashawa da cin hanci wanda ya shafi duk masu ruwa da tsaki.

Farfesa Adamu A. Rasheed
%d bloggers like this: