Lantarki Ta Hallaka Fursunoni Masu Yawa A Gidan Kurkukun Ikoyi

  • Home
  • Labarai
  • Lantarki Ta Hallaka Fursunoni Masu Yawa A Gidan Kurkukun Ikoyi

Daga Yaseer Kallah

Rahotanni sun bayyana cewa an samu hadarin wutar lantarki a gidan kurkukun Ikoyi, wanda yake babbar cibiyar gyara halinka ta jihar Legas.

Rahotannin sun bayyana cewa fursunoni da dama sun rasa ransu, wasu kuma sun samu raunuka a lokacin da wayoyin lantarkin gidan suka kama da wuta a cikin safiyar ranar Litinin.

Babban kakakin hukumar gyara halinka ta Nijeriya, Francis Enobore, ya tabbatar wa majiyarmu ta PREMIUM TIMES afkuwar hadarin, amma ya ce suna nan suna tattara jawabi kafin su bayyana wa al’umma cikakken rahoton.

Gidan kurkukun Ikoyi na daya daga cikin tsofaffi kuma mafi girman gidajen gyara halinka da ke dauke da dubunnan fursunoni.

%d bloggers like this: