DALILINA NA YIN RUBUCE-RUBUCE A FANNONI-HELON HABILA

  • Home
  • Labarai
  • DALILINA NA YIN RUBUCE-RUBUCE A FANNONI-HELON HABILA

Helon Habila Farfesa ne a bangeren rubuce-rubuce na kirkira a Jamiar George Mason dake kasar Amurka. Marubucin littattafai ne da suka kunshi Waiting for an Angel da Measuring Time, da Oil on Water, da The Chibok Girls, sai kuma na baya-baya nan Travelers wanda ya fitar bayan tattaunawa da bakin haure da yan hijira. A wannan hira da ya yi da Weekend Magazine, ya fadi abubuwan da suka ja hankalinsa a rubutu, sannan ya yi bayani akan sabon littafinsa da harkar koyarwa da yake a Amurka da sauransu.

Helon Habila

Amon Nasara: Me yasa sabon littafinka Travelers ya bada mihimmanci akan yan hijira?

Helon Habila: Na rubuta shi ne saboda daliliai masu yawa. Na farko alamari ne da ya zama abin tattaunawa a duniya, ni kuma na kasance mai shaawar duban irin wadannan alamura da suka zamo ababan muhawara. Za ka ga hakan a littattafaina na baya-baya Oil on Water da wanda ba na kirkira ba a kan Boko Haram. Ina shaawar yin rubutu a ire-iren wadannan bangarori, domin na fahimci suna da mihimmanci. Za ka iya gane inda alummar da kake ciki ta dosa, da magance ire-iren matsalolinta. Za ka iya zurfafawa ta hanyar duba na tsanake ga taurarinka tare da laakari da siyasa da kulunbiton dake tattare da abubuwan da suka zamo abin tattaunawa a yau da kullum. Don haka ina da shaawar kallon labaraina ta wannan fuska. Ina farawa da abubuwan da suka zamo abin tattaunawa na yau da kullum, sannan na zurfafa tunani. Ina kokarin nunawa mutane abin da ba sa gani, kasancewar irin wadannan abubuwa sun zama na yau da kullum. Misali, na kasance a kasar Jamus na tsawon shekara don rubuta Travelers. Ina can a shekara ta 2013 aka samu wani hadarin karamin jirgin ruwa da ya nutse a cikin tekun Mediterranean, kusan yan hijira 300 suka mutu. To sai wani kamfanin jarida a can Jamus ya nemi na rubuta wani abu akai kasancewata marubuci dan Afirka, tunda ya kasance mafi yawan wadanda ke cikin jirgin ruwa yan Afirka ne. Duk da cewa na san abubuwa a kan yan gudun hijira na Afirka, amma dole sai da na tattauna da masu gudun hijirar da yawa, saboda wannan shi ne karo na farko da zan yi rubutu a wannan fanni. Wannan ne ya bani dama na fahimci akwai labarai a cikin alamarin, amma muna samun wani dan birbishi ko kanu ne daga jaridu. Abu ne da za a iya yi musu uziri, kasancewar ba su da isashshen lokaci da za su kawo cikakken labari. Da zarar na yi magana da mutane, sai na ji bukatar na buda bayani sosai. Ina son kawo bayani kamar yadda suka gani da idonsu, sannan ina son masu karatu su ma su gani kamar yadda suka gani. Ba wai kawai kawo kididdiga ba ko magana akan yan gudun hijira, su ma mutane kamar kowa. Wannan ne ya ja raayina na fada abin da ya shafi Matafiya.

AN: Ka kan fuskanci matsala yayin juya labaran da ka nado zuwa rubutun kirkira ko wanda ba na kirkira ba?

Habila: Aa, na san me nake so na yi. Ina son kawo muryoyinsu kamar yadda suka fada mun labaransu, sannan ina kokarin tabbatar da ingancin labaran. Bana son sauya abubuwa da yawa. Amma dole na sauya wasu don mayar da shi kamar yadda yake a yanzu. Na fahimci cewa a kowanne lokaci ni mai bada labari ne. A kirkirarren labari, kana da rawa da za ka taka a kan taurarinka ta yadda za ka bada hotonsu ga mai karatunka har ya fahimce su sosai ba wai a matsayin matafiya kawai ba. Na kira su matafiya maimakon masu hijira, saboda ba na son mai karatu ya yi saurin gano ina labarina ya dosa. Kuma ba dukkan taurarin littafin ba ne yan hijira. Babban tauraron ya fito daga Amurka ne, kuma ba dan hijira ba ne. Hakazalika matarsa ma ba yar hijira ba ce. Kawai matafiya ne. Na yi kokarin samar da wani tauraro da zai goya labaran sauran taurarin. A gaskiya abu ne mai matukar wahala a fasahance. Misali, yadda zan juya wannan labari da ba kirkirrarre ba zuwa tsarin labari mai nishadantarwa, wanda yake dauke da salo da zubi, sannan aka tsara shi a kasashe na daban, a Jamus da Switzerland da London da sauransu. Dole na samar da tauraro da zai iya shiga ya yi tasiru a dukkan labaran cikin sauki da gamsarwa. A lokaci guda ina so ya zama akan Najeriya, saboda littafi ne na Najeriya. Duk da cewa shi ne littafina na farko da aka gina shi a inda ba a Najeriya ba. Don haka nake son jigonsa ya zamo ta mahangar Najeriya. Wannan ne yasa na zabi wani dalibi da yake karatun digirinsa na uku (PhD) a Amurka, inda ya auri wata mata kwararra a harkar kirkira (artist) Matar ta samu tallafi da gurbin karo karatu a Jamus, wannan ne yasa suka taho tare.

AN: Kai ma ka samu tallafin karatu a Jamus

Habila: Eh. Na je can don na rubuta wani littafi amma sai na kare da rubuta wani na daban. Ban taba tsammanin zan rubuta Travelers lokacin da na je Jamus. Yanzu ina kokarin kammala ainahin littafin da na je Jamus don na rubuta. Lokacin da na fara rubuta Travelers a 2013 zuwa 2014, dole sai da na jingine rubutun don na rubuta littafin Boko Haram, kafin daga baya na dawo na karasa. Na dauki tsawon shekaru biyar kafin na gama rubuta Travelers, saboda ina gudanar da bincike. Sannan ina son mutanen da na tattauna da su su karanta abin da nake rubutawa su bani raayinsu akai, domin ba na son kawo abin da ba raayinsu ba ne, ko ya zama abin wulakanci. Don haka na tura musu kwafin farko na labarin, wanda suka yi farin ciki da shi sosai bayan sun karanta. Wannan na daya daga cikin dalilan da yasa na dauki lokaci mai tsawo.

AN: Akwai wasu maaurata da suka rabu a cikin labarin. Kana ganin karshen labarin a haka ya yi wa masu hijirar dadi?
Habila: Gaba daya labarin yana magane ne akan rabuwa. Har rabuwar ta zamo kamar wani zaurance ne na tafiya. Ta wata fuska kuma magana ce ta yin rashi da yawa. Da farko sun rasa gidajensu dake kasashensu sannan sun rasa shaidarsu na yan kasa. Don haka suna kokarin yadda za su dawo da martabar su ne a sababbin gurare da suka sauka. Ba wai kawai akan iyalinsu da suka rabu dasu ba ne. Akwai wani tauraro dan kasar Somali da ya rasa dansa domin ya fada addini kiristanci. A takaice yana magana ne akan yadda ake yin rashin abubuwa. Ko auren da wani tauraro dan Najeriya da ba a ambaci sunansa ba ya yi, abin ya kare cikin halin kakanikayi. Ka kan rasa abubuwa da yawa idan ka yi kaura zuwa sabon guri. Wani lokaci ba abubuwa ba ne da za ka gani baro-baro. Za ka rasa iyalinka da matsayinka a duniya, wanda dole sai ka yi kokarin samawa kanka kima da daraja a sabon gurin da ka sauka. Kamar kana kokarin gina sabuwar rayuwa ce tare ganin ka saje a cikin sabuwar rayuwar da ka tsinci kanka. Don haka za a iya cewa rayuwa ce da ta shafi rashi. Kokarin bayyana yadda wannan rashin yake, zai kara haske dangane da fahimtar yadda rabuwa da iyali yake.

AN: Me za ka ce game da abin da ya fi ba ka kalubale yayin rubuta Travelers?
Habila: Abin da ya fi bani kalubale shi ne yadda zan juya labarin da yake na gaskiya ne zuwa kirkirarren alamari ta yadda zai nishadantar da masu karatu ya kuma basu shaawa. Domin ni marubuci ne mai bada labarai tare da rubuta littattafai na kirkira da za su sanya makarantana jin dadi da gamsuwa. Ina son jan hankalinsu, domin na rike makaranta, saboda dadin abin da suke karantawa zai sa su fahimci littafin da ainahin abin da nake son cewa. Abubuwa da suka shafi irin wannan kan gunduri mai karatu wani lokaci, wannan yasa dole na tabbatar ya kayatar. Hanyoyin da zan bi don cimma wannan manufa ita ce taurarina da harshen da na yi amfani da shi. Dole na yi rubutu mai kyau tare da salon bayani da zai ba ka hoton inda taurarina suka nufa. Wadannan na daga cikin abubuwan jan hankali da yakamata na kawo domin jan zaren labarin cikin ban shaawa.

AN: Lokacin da ka kudiri niyyar rubuta littafinka na karshe, The Chibok girls, wane irin salo ka yi amfani da shi da ya banbanta da na sauran?
Habila: Saboda wani ya yi rubutu akai ba zai hana ni yin nawa ba. Yawan rubuce-rubecen mu shi zai ba mu cikakkiyar fahimta akan matsalar, domin kowa na da tasa mahangar a rayuwa. Ni kirista ne da ya fito daga yankin arewa, sannan wannan alamari na faruwa ne a kusa da mahaifata, a yankin arewa maso gabas. Kamar ina cikin labarin ne dumu-dumu don kokarin bayar da tawa fahimtar. Ta yu wani ya yi rubutu a kai daga bangaren kudu ko kuma ta mahangar musulmi dan arewa. Ina kokarin fahimtar ainahin abu, ina rubutu ina kuma yin bincike. Hakan yasa na je Chibok na tattauna da wasu daga cikin yaran tare da iyayensu domin na samu fayyace wasu abubuwa. Najeriya ta sauya sosai. Na bar kasar shekaru goma sha bakwai da suka wuce. Lokacin da samu labarin Boko Haram, sai abin ya zamar mani kamar wata kasa ce ta daban, ba Gomben da sani ba a baya ba. Ina da yan uwa da suke musulmi kuma muna zaune cikin kwanciyar hankali. Amma yanzu sai rikice-rikece da sunan addini. Ina son fahimtar ainahin lamarin don na iya gaya mutane gaskiyar abin da yake faruwa. Hanya mafi sauki da zan iya haka ita ce ta rubutuna.

AN: Ta ya ya kaura da ka yi zuwa Amurka ta yi tasiri a rubutunka?
Habila: Abu ne da yake sauyawa lokaci zuwa lokaci. Ina yin rubutu iri-iri, sabanin da a ce ban bar Najeriya ba. A matsayinka na marubuci kana samun sauyi, saboda mahalli da ka sauya. Hakan yana da tasiri ga fahimtarka a duniyance. Ta haka za ka iya fahimtar yadda wasu abubuwa suke gudana. Kamar ka kallin kanka ne bayan ka fita daga dairar Najeriya. Hakan zai ba ka dama ka kalli abu a tsanake kuma ta kowanne bangare. Don haka sai na samu damar kallon kasar tare da danganta ta da Amurka da sauransu a matsayin wanda ba a cikinta yake ba. Na shiga wani hali na kadaici sosai. Wani lokaci akwai damuwa idan aka ce ba ka kasarka, akwai kadaici da tunanin abokai da yan uwa da ka bari. A shekarata ta farko a Amurka, na kusan samun ciwon mutuwar barin jiki, saboda na kasa tunanin wani abu da zan iya rubutu a kai. To me zan rubuta? Zan rubuta abin da ya shafi Najeriya ne ko Amurka? Idan akan Najeriya ne, to me zan rubuta? Wannan ne yasa na rubuta Oil on Water. Wani kamfanin shirya finafinai ne ya tuntube ni da na yi musu rubutu akan garkuwa da mutane a Niger Delta. Wannan shi ya ja hankalina na rubuta Oil on Water. Bayan wannan littafin sai na cigaba da yin wasu rubuce-rubucen. Amma tsakanin Measuring Time da sauransu, ba abin da nake rubutuwa. Amman na yi littafin Hadaka na gajerun labarai, wanda ba dukkan su ba ne ainahin ayyukana, domin na kara na mutane. Na kasance wanda ya tattaro labarai daga sauran mutane. Irin wannan ne zai faru da kai a matsayin marubuci idan ka bar inda ka taso. Abin na da matukar wahala, sai dai zai fi kyau idan ka iya daurewa daga kadaici da damuwar da kake ciki. A yanda ake dauka shi ne idan kana zaune a Amurka, to ba ka da matsala. Eh, kana da komai a can, amma kuma akwai fargaba da damuwa da yawa. Dole ka sauya abincinka, sannan ana kallonka a matsayin wani mutum na daban. Don haka dole sai ka samarwa kanka mafita a cikin sauran mutane. Abin ya zo mun da sauki kasancewar ina tare da matata da yayana. Ita ma kuma yar Najeriya ce, hakan ya taimaka sosai. Amma dai mutum zai rasa abokai da yan uwa, wanda hakan sai ya yi tasiri a rubutunsa.

AN: Kai Farfesa ne na rubutun kirkira a Jamiar George Mason. Ya ya koyar da dalibai yake a can?

Habila: Abu ne mai matukar ban shaawa. Wani lokacin na kan kasance bakin mutum tilo a ajin. Amma ina cike da farin ciki tare da gabatar musu da rubuce-rubucen Afrika. Ina kokarin ganin na kawo musu da gajerun labarai da litattafai na kirkirarrun labarai masu yawa, wanda ba lalle bane su taba karo da su idan da bana nan. Don haka ina kallon kaina a matsayin wanda yake bude musu idanu idan aka zo magana akan fahimtar adabi. Amurka wata cibiya ce ta duniya, amma za ka sha mamaki cewa da yawansu ba su san mai duniya ke ciki ba, musamman matasa da ba su taba samun damar yin tafiye-tafiye ba. Ina ganin zai fi kyau a matsayinsu na marubuta su fahimci aladun wasu. Akwai rubuce-rubuce masu yawa akan aladu wanda Afirka na da tarinsu.

AN: Akan mene ne rubutunka na gaba yake magana?
Habila: Bana son na camfi labarin. Don wani lokacin na kan camfi abu. Amma dai zai kayatar sosai fiye da na baya. Littafin da nake rubutawa yanzu shi ne na so a ce na rubuta shi kafin na rubuta Travelers. A halin yanzu ina kan yi masa kwaskwarima. Ina fatan nan da shekara biyu zai fito.

An ruwayo daga mujallar Weekend Magazine.

%d bloggers like this: