KOTU TA RUSHE MASARAUTU HUDU DA GANDUJE YA KIRKIRA

  • Home
  • Labarai
  • KOTU TA RUSHE MASARAUTU HUDU DA GANDUJE YA KIRKIRA

Babbar kotu a jihar Kano karkashin mai shari’a Usman Na’Abba ta rushe sababbin masarautu guda hudu tare da sarakunansu masu daraja ta daya da gwamnatin Kano ta kirkira.


Idan ba a manta ba, a ranar 8 ga Watan Mayu ne gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar kudirin kirkiro da sababbin masarautu guda hudu a Kano tare da sarakunansu masu daraja ta daya a Bichi da Rano da Karaye da Gaya. Sannan a watan na Mayu gwamnan Kano ya bada takardar kama aiki ga sababbin sarakunan.


Rahoton da Amon Nasara ta Samu ta hannun jaridar Daily Nigerian ya ruwaito cewa gwamnan Kanon ne ya shigar da wannan kudiri majalisa ta yin banda bami da sunan wani can. An bayyana cewa wani lauya mai suna Ibrahim Salisu ne ya fara gabatar da bukatar kirkirar sababbin masarautun a Kano da sunan kamfaninsa. Sai kawai aka wayi gari majalisa ta jihar Kano ta yi zama don tabbatar da wannan doka.


Yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis, kotun ta bayyana cewa majalisar jihar Kano ta karya ka’idar sashi na 101 na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa gyara a shekara ta 1999.


A cewarsa hanyoyin da aka bi wajen gabatarwa tare da gyaran dokar ya saba da doka, don haka duk wani hukunci da mataki da aka dauka yayin zaman gabatar da kudirin rushashshe ne.


Don haka ya aiyana dokar da ta tabbatar da samar da masarautun a matsayin wanda ba ta da tushe bare makama. Daga wannan hukunci za a iya cewa Sarki daya ne a Kano.


Amma lauyan gwamnatin jihar Kano Barista Ibrahim Mukhtar ya shaidawa ‘yan jarida cewa kotu ta yanke hukuncin ne ba tare da tsayawa ta yi bincike sosai ba.


Tun farkon shari’ar dai tsohon shugaban marasa rinjaye na malisar ta Kano, Nasiru Muhammad Gwarzo ne ya shigar da kara kotu yana kalubalantar dokar majalisar da yadda aka gabatar da ita.
Shi ma lauyan mai kara Maliki Kuliya ya nuna farin cikinsa da hukunci, inda ya ce kotu ta yi abin da ya dace.

%d bloggers like this: