KISHIN KASA, TUSHEN CIGABA DA BUNKASA


A kwanakin baya na yi rubutu mai taken A DA A NAJERIYA AN BI DOKA DA ODA, inda na kawo yadda kasar Najeriya ta ke a duniya kafin matsaloli sun kwantar da ita. Tabbas muna cikin matsala, amma hakan ba yana nufin mun yanke kauna da samun sauki ko fita daga cikin wannan hali ba. Hakika jarrabawa ce wanda za mu iya cinta idan mun koma ga Allah, sannan muka gyara halayen mu.
Babban abin da ya kamata mu fara yi shi ne mu sa kishi da son kasarmu a saman komai. Ba mu da wata kasa da ta fi Najeriya, anan muke rayuwa, anan iyayenmu da kakanninmu suka rayu, sannan anan ‘ya’ya da jikokinmu za su rayu. Babu inda za mu je idan ba ma kishin kasarmu. Kishi kasa shi ne zai sa ka ga wani abu zai faru na cutarwa ga kasarka ka yi amfani da karfinka ka dakile shi. Wannan ne dalilin da yasa ko yaki ne ya tashi, ya zama wajibi ko ana so ko ba a so mutanen kasa su dau makamai don kare kasarsu. Kishin kasa ne kan sa mutum yake hakura da jin dadi ko wata alfarma ta duniya matukar kima da daraja ta kasarsa za ta tabu. Kishin kasa ke sanya soja ya bar iyalinsa tare da masoyansa ya tafi uwa duniya inda zai iya rasa ransa don kawai kasarsa ta zauna lafiya. Kishin kasa ne kansa a yau idan a duniya aka ambaci wata mummunar kalma ga kasarka ka ke jin daci a ranka, har ka fito ka nuna rashin jin dadinka.
Wani zai iya cewa to ita mai kasar ta yi mun da zan bada rayuwata a kanta. Amsar ita ce, ai ita kasar ba ita ke juya kanta ba, asali ma ‘ya’yanta ne suke juya komai na ta. Ashe idan aka ga wani abu da ba daidai ba, rashin tunani ne a daura laifin a kan kasar, fashe ‘ya’yanta da suke jan ragamar gudanarwa. Idan har matsaloli sun dabaibaye kasa, ba ido yakamata a zuba ba. ‘Ya’yan wannan kasar yakamata su zauna daga dattawa zuwa matasa su rungumi wannan matsala don fito da mafita. Wannan kuwa ba zai yu ba sai akwai kishi da kaunar kasar. Muna kallon kasashe da yawa a duniya walau a Turai ko Asia da sauran nahiyoyi da suka cigaba, muna sha’awarsu tare da yaba tsarinsu. Amma kuma mun san cewa ba haka aka wayi gari suka zama yadda suke ba. Sai da suka fitar da tsari sannan suka tabbatar da bin wannan tsarin. Na yi imanin ba cikin sauki suka samu wannan nasara ba, sai da suka yi aiki tukuru da jajircewa. Shi kuma aiki tukuru da jajircewa ba za su samu ba sai ka yarda da abin da kasa a gaba, sai ka yi imani cewa wannan abin shi ne mafita a gareka.
Shin ta ya ya zamu dawo da kishin kasa ta yadda za mu kudurce a zuciya kasarmu Najeriya tana gaba da komai? Da farko dai sai mun koma ga matasanmu, domin sune tubali na cigaba daga al’umma zuwa al’umma. Ya zama dole yara tun daga makarantu na Firamare a nuna musu mihimmancin kasarsu. Lokacin muna firamare a duk safiya sai mun hadu an yi addu’a, wanda jigon addu’ar fata ne da rokon Allah ya albarkaci kasar tare da rokon Allah ya bamu ilimi mai amfani, wanda zai kasance cikin soyayyar manzon tsira Annabi Muhammadu S.A.W tare da bin dokokin Allah. Har yanzu ina iya tuna wadannan addu’oi da muke cikin wake. Na tabbata ba za su tafi a banza ba. Sai dai abin bakin ciki a yanzu an yi watsi da su, musamman yanzu da aka samu makarantu masu zaman kansu. Za a iya cewa a yanzu sai abin da malamai suka ga dama, asalima wasu wakoki da ake gabatarwa ba su da nasaba da addininmu ko al’ada. Idan muna son kishin kasa sai mun dawo da wadannan abubuwa.
Ya zama wajibi idan muna son bunkasa da cigaba, a cikin darussan da muke koyarwa ga ‘ya’yanmu a sanya wadanda za su nusar da su kishin kasa da taimakekeniya. Dole a wannan mataki a ba su mihimmanci, domin mataki ne na gina rayuwa. Hausawa na cewa Icce tun yana danye ake tankwara shi. Kuma tun ran gini tun ran zane, babu lokacin da ya dace mu ba yara tarbiyya kamar wannan lokaci.
Yayin da ka bada tarbiyya kana sa ran samun kyakykyawan sakamako. Idan har aka samu wadanda suka kauce hanya, mafita shi ne a samar da hanyar horo. Shi dama Dan Adam ba lalle ba ne dari bisa dari ya zamo mai kiyaye wa ba. Babban abin da zai dawo da shi hanya idan ya kauce, shi ne horo. Wanda kuma ya dore da kyawawan dabi’u, shi kuma dole a yaba masa ta hanyoyi da dama da aka tanada.

Sir Ahmadu Bello yayin ziyartar makaranta

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

%d bloggers like this: