RUFE BODA: IDAN AN CIZA A HURA

Duk da na ambaci irin amfani da hanyoyin da za a bi wajen cimma nasara a rufe bodar da gwamnati ta yi, ya dace kuma na duba daya bangaren abin da ka je ya zo.

Da yake mahukunta na buga misali da kasar China lokacin da ta rufe iyakokinta, bari mu leka kundin tarihi mu gano.
China ta saba da rufe iyakokinta tun fil azal. Akwai wata babbar hanya da ake kira Silk Road, ta soma tun daga China ta zagaya sassan duniya da dama har zuwa Afrika da turai da larabawa da sauransu. Ta nan fatake suke bi zuwa China su yi fataucin siliki da sauran abubuwa. Wannan hanya tana dumbin tarihi na cinikayya da siyasa da yaki da sauransu.
Idan China ta ga dama sai kurum ta rufe wannan hanya ta hana a ratsa ta kasar ta. Sai an dauki lokaci ana bata kashi sannan su bude a cigaba da kasuwanci. Suna cewa dalilan su na rufe iyakokinsu domin su samu zarafin gudanar da ayyukansu ne kada a kawo musu bakin al’adu. Kuma suna ganin ba sa bukatar komai tunda a wajensu ake nema ba su ne ke nema ba.

Cikin 1949 suka sake rufe iyakokinsu inda suka maida hankali ga aikin gona da masa’antu. Duk da haka akwai kasashen da suke dasawa da su har suna cinikayya tsakaninsu. Babbar kawar China a wancan lokacin ita ce Rasha, wadda ra’ayinsu ya zo daya akan mulkin kwaminisanci. A wannan tsakanin kuwa an ce miliyoyin mutane sun saboda yunwa da kisan shugabanni da kuma masu kashe kansu da kansu.

Bayan mutuwar Chairman Mao, sai shugabannin jam’iyyar su ta kwaminisanci ta yi karatun ta nutsu, suka duba irin illolin da yanke kansu daga duniya ya haifar da irin nasarorin da aka samu. Suka ga cewar talakawa sun fadaka kuma sun zama jajirtattu, sannan shugabanni sun maida hankali ga ceton kasarsu. Don haka a 1978 cikin watan Disamba, Shugaba Deng Xiaoping ya sanar da juyin juya hali na cinikayya da tattalin arziki.
Nan da nan mutanen kasar suka dukufa wajen aiki ba kama hannu yaro, hukumomi suka tashi haikan wajen tabbatar da abin da suka ayyana za su yi. Don haka ya zamana an samu gagarumin canji. An ce a shekarar 1980, adadin matalauta a China ya kai 88%, amma a 2017 ya koma kasa da 6% wadanda ke samun dala 2 kullum.

SABUWAR DABARA
Cikin shekarar 2012 China suka ga kamar tattalin arzikinsu yana ja da baya saboda shigar ‘yan kasuwa da sauran mazambata cikin kasar su. Wasu daga cikin mashawartan gwamnati suna da ra’ayin a koma ‘yar gidan jiya a rufe iyakokin kasar a cigaba da aiki irin yadda aka saba. Nan take aka ruguza wannan ra’ayi da cewa ya zama tsohon yayi musamman irin mukamin da China ta samu a duniya kasancewar ta lambatu a karfin tattalin arziki da fada aji.

Cikin watan Mayu na 2015 Shugaba Firimiya Li Keqiang, ya kaddamar da wani tsari da ake kira ‘Made In China 2025’. A karkashin wannan sabuwar dabara ana so China ta zama lambawan wajen samar da ingantattun kayayyakin a kowanne fanni ta hanyar amfani da fasahar zamani da kuma robot kafin 2025. Tuni gwamnatin ta ware dala biliyan 300 domin aiwatar da wannan tsari.

An dauki nauyin yara da yawa an kai su kasashen duniya domin karatu mai zurfi na fasahar zamani da kirkira. Kuma duk wanda yayi bajinta gwamnati na daukar nauyinsa tare da tallafa masa. Tuni dai shirin yayi nisa kuma sun soma ganin amfaninsa. Kodayake duniya tayi musa ca akan cewar sun taka wasu dokokin cinikayya ta duniya.

Ba kasar China ce kadai ta rungumi sabuwar dabarar habaka tattalin arzikin ta ba, kasar Jamus na da tsarin da ake kira ‘Industry 4.0,’ Japan tuni ta yi nisa wajen kirkira ta amfani da dabaru masu yawa. Amma mu a Nijeriya an bar mu da rikici kan shinkafa mai tsakuwa da mai manja. Kaico!
Daga wannan waiwaye za mu nakalci abubuwa da dama kamar haka;

a. Dabi’ar shugabannin China ne tun fil azal su rufe iyakokinsu da zarar sun ga haza.
b. Shugabannin siyasar China sun fi na Nijeriya dadewa da karagar mulki, don haka suke iya kaiwa bantensu.

c. Shugabannin China sun fi na Nijeriya kishin kasarsu da kokarin samar mata da mafita.

d. Talakawan China sun fi na Nijeriya biyayya da hakuri.
e. Rufe boda tsohon yayi ne bisa zantukan masana, amma akwai hanyoyin da ake iya magance matsalar kasa ba tare da an garkame kofa ba.

Wadanne hanyoyi ne za a iya amfani da su wajen magance matsalar gibin tattalin arziki ba tare da an rufe boda ba?
Rubutuna na gaba zai yi tsokaci kan haka da yardar Allah.

%d bloggers like this: