Yadda Manyan Nijeriya Ke Bayyana A Gaban Kotu A Kan Kekunan Guragu Da Gadajen Asibiti

  • Home
  • Labarai
  • Yadda Manyan Nijeriya Ke Bayyana A Gaban Kotu A Kan Kekunan Guragu Da Gadajen Asibiti

Yadda Manyan Nijeriya Ke Bayyana A Gaban Kotu A Kan Kekunan Guragu Da Gadajen Asibiti

‘Yan Nijeriya sun jima suna mamakin yadda wasu manyan Nijeriya ke gurfana a gaban kuliya a kan kekunan guragu, gadajen asibiti ko rike da sandar guragu, alhali kafin kotun ta neme su tsaye suke kyam a kan kafafunsu. Shin hakan wani sabon salo ne na neman kotu ta tausaya masu ko kuma lalurar ce ta gaske?

Amon Nasara ta zakulo wasu daga cikin manyan Nijeriya da suka gurfana a gaban kuliya da irin wannan salon.

Abdulrasheed Maina

Abdurrasheed Maina bisa keken guragu

Abdurrasheed Maina ya kasance tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul. A yanzu haka babbar kotun tarayya da ke Abuja na tuhumar sa a kan zargin almundahanar naira biliyan biyu. A ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, 2019, Maina ya gurfana a gaban kotun a kan keken guragu inda lauyoyinsa suka yi ikirarin yana fama da rashin lafiya. Saidai kuma ba Maina ba ne kawai ya taba gurfana a gaban kotu a haka ba.

Halliru Muhammad

Halliru Muhammad

A watan Junairu, 2016, tsohon shugaban jam’iyar PDP na kasa, Halliru Muhammad, ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan keken guragu biyo bayan zargin da ake masa na taka rawa a cikin cin kudin makamai.

Patrick Akpobolokemi

Patrick Akpobolokemi

A watan Maris, 2016, tsohon daraktan hukumar kula da sufurin jiragen ruwa, NIMASA, Patrick Akpobolokemi, ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya rike da sandar guragu domin fuskantar tuhuma a kan laifin almundahana da kudin kasa.

Chief Olisah Metuh

Chief Olisah Metuh

A watan Maris, 2018, tsohon sakataren yada labaran jam’iyar PDP na kasa, Olisah Metuh, ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya ta birnin Abuja a kan keken guragu domin ci gaban tuhumar da kotun ke masa a kan laifin rashawa.

Sanata Dino Melaye

Sanata Dino Melaye bisa gadon asibiti

A cikin watan Mayu, 2018, Dino Melaye, sanatan da ke wakiltar Kogi ta yamma, ya gurfana a gaban babbar kotun majistare da ke Abuja kwance a kan gadon asibiti, sakamakon yunkurin kashe kansa da ya yi ta hanyar tsalle daga cikin motar da za ta kai shi Lokoja domin fuskantar tuhuma a kan wani laifin ta’addanci.

Manjo Janar Hakeem Otiki

Manjo Janar Hakeem Otiki

A watan Satumba, 2019, Manjo Janar Hakeem Otiki, babban kwamandan rundunar mayaka ta 8, ya bayyana a gaban babbar kotun soji bisa keken guragu sakamakon zargin karkatar da makudan kudade da suka kai kimanin naira miliyan 400 zuwa 600.

%d bloggers like this: