EFCC Ta Kwato Motoci Daga Hannun Shugabannin Jami’ar Dutsin-ma

  • Home
  • Labarai
  • EFCC Ta Kwato Motoci Daga Hannun Shugabannin Jami’ar Dutsin-ma

EFCC Ta Kwato Motoci Daga Hannun Shugabannin Jami’ar Dutsin-ma

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ofishin shiyar Kaduna, ta damka wasu motaci guda hudu da ta karbo daga hannun wasu shuwagabannin jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-ma, jihar Katsina, ga hukumar jami’ar.

Kakakin hukumar, Mista Wilson Uwujare, ya bayyana cewa karbar motocin ya biyo bayan wata takardar koke da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya aike wa hukumar, inda yake zargin cewa tsofaffin shuwagabannin jami’ar sun shaka wa aljihunansu wasu miliyoyin naira a matsayin alawus din aje aiki tare da yin wata mu’amala ta kudi mai cike da abubuwan zargi da wani babban banki. Shuwagabannin jami’ar su ne: Farfesa James O. I. Ayatse, shugaban jami’a; Muhammad Yusuf Abubakar, Rajistara; da Sadiq Momoh Jimoh, Ma’aji.

Uwajare ya ce wasu daga cikin zargin da ke kansu sun hada da saya wa kansu wasu abubuwa a kan farashi mai matukar tsada da kuma saba ka’ida a gurin bayar da kwangiloli.

Motocin da hukumar ta karbo sun hada da motoci kirar Toyota Corolla guda biyu masu lambar FUDMA 51F -03FG da FUDMA 51F-05FG; Toyota Land Cruiser ZTRJ150L mai lamba FG 668 – E45 da Toyota Camry XLE 205 mai lambar ABC 601 LX.

Yayin da ake bikin maido wa jami’ar motocin, shugaban hukumar na shiyar Kaduna, Mailafia Yakubu, ya bayyana cewa an saki motocin biyo bayan rokon da hukumar jami’ar ta yi domin ta samu saukin tafiyar da harkokin jami’ar.

Ya ce, “damka wa jami’ar motocin shaida ce da ke nuna cewa yaki da rashawa da cin hanci gaskiya ne, sannan ana nan ana kara gabatar da bincike, kuma za a gurfanar da wadanda abun ya shafa a gaban kuliya.”

A dangane da jawabin Uwajaren, sabon rajistaran jami’ar, Aliyu Kankia, ya bayyana cewa maido wa jami’ar motocin zai saukaka kalubalen sufurin da jami’ar ke fuskanta.

%d bloggers like this: