DA ZA A RUFE BODA KAMAR SHEKARA BIYU BILHAKKI….

  • Home
  • Labarai
  • DA ZA A RUFE BODA KAMAR SHEKARA BIYU BILHAKKI….

Daga Danladi Haruna

Kafin na amsa abin da nake nufi a sama, bari na yi tsokaci kan wasu abubuwa da ake la’akari da su a cinikin kasa da kasa.

Masana tattalin arziki suna kiran kudaden da kasa ke samu daga saye da sayarwa ‘Balance of Payment’. Ana kiddidige yawan kudin da kasa ta samu sakamakon fitar da kayayyaki da sana’a da sauransu zuwa kasashen waje. Haka kuma ana lissafa abin da aka samu a wajen sayo kayayyakin daga waje. Abin da aka fitar waje shi ne ‘Export’ wanda ke matsayin kudin shiga. Abin da aka shigo da shi ana kiransa ‘Import’. Yana matsayin kudaden da suka zurare.

Idan kudin Export ya zama daidai da Import to an samu kunnen doki kenan. Idan kuma Export ya fi Import yawa, to an samu rara kenan wanda hakan ke nufin cigaban arziki. Haka kuma idan Import ya fi Export yawa to an samu nakasu kenan wanda haka ke nufi ci baya.

Akwai matakan da kasa ke dauka domin tabbatar da ta samu rara ko kunnen doki a Balance of Payment din ta. Wasu daga ciki sun hada da, tsaurara hanyoyin shigo da kaya da kuma saukaka fitarwa, karya farashin kudin gida, janye kudi daga hannun mutane, hana bashi, kara yawan kudin ruwa, cin bashi da kuma inganta masana’antun cikin gida.
Wasu daga matakan da na ambata din nan suna da kyau sosai, wasu kuma suna jawo kara tabarbarewar abubuwa. Misali janye kudi ko karya darajar su, yana jawo haihuwar guzuma. Talauci da babu da hauhawar farashi na iya aukuwa. Don haka wajibin kasa ne ta rika bin matakan sannu – sannu.

A Nijeriya, tun daga 1981 har zuwa 2015 ba a taba samun kunnen doki a Balance of Payment sai sau uku. Shekarun su ne, 1985, 1986 da kuma 1990 wanda ya samu sakamakon rufe boda da kara harajin shigo da kayayyaki. Duk da hakan bai haifar da da mai ido ba, sai ma kara jefa jama’a cikin kunci.

Bari mu sake waiwayawa baya, a zamanin Shagari Nijeriya ta fada rikicin tattalin arziki sakamakon karyewar farashin man fetur. Saboda haka gwamnatin ta samar da dokar tada komadar tattalin arziki wadda ta saka takunkumi ga wasu kayayyakin da ake shigowa da su. Da Buhari ya hau mulki a 1983, sai ya karawa dokar nan karfi inda aka rufe boda kuma aka matsantawa masu shigo da kayayyaki.

To amma Babangida na hawa sai ya bude boda tare da kakaba harajin shigo da kaya zuwa 30% saboda yana so a saba da tsarin kowa ya ji a jikinsa wanda ake kira SAP a takaice. Sai dai hakan bai taimaka da komai ba sai sake shiga wata matsalar ta hauhawar farashi. Shi kuwa Abacha da yake gwamnatinsa bata yi farin jini ga ‘yan siyasa ba, sai ya takurawa kowa inda aka maida harajin fito zuwa 100% har da doriya ga wasu abubuwan. Nan ma dai sai kasar ta sake dagulewa daga mai jin kishirwa zuwa mayunwaciya.

Abubuwa sun sake tabarbarewa ne a zamanin farar hula, duk da ikirarin da Shugaba Obasanjo yayi na rufe boda da dakile fasa kwauri da farautar mahandama. Sai ya kasance ana kamun kafa ga manyan ‘yan siyasa ana shigo da kaya bisa alfarma. Wasu abubuwan ma, Obasanjo da kansa yake bada umarnin shigo da su saboda na manyan hamshakai ne.
Haka aka cigaba da yi a zamanin ‘Yar Adua domin an ce hatta wasu ministocinsa suna zuwa neman alfarmar yafe kudin haraji ga wasu kayan. Shi kuwa Jonathan duk da kirarin da ya sha yi na hana shigo da kayyayaki, sai ya zamana manyan ministocin sa ma na cikin wadanda ke shigo da su tare da banga-banga wajen kara wa Barno Dawaki.

Ashe kenan ba tun yanzu ake ta fafutukar sarrafa shigo da kaya cikin kasar Nijeriya ba domin a samu daidaito a Balance of Payment watau musayen cinikayya tsakanin kasashen duniya.

Masana sun bayyana cewar manyan dalilan da suka jawo aka kasa cimma manufa su ne; na farko alfarma da cin hanci wadanda aka maida su farilla da sunan ‘waiver’. Na biyu masu fasa kwauri da ɗamfare a bakin boda wadanda suka zama kadangaren bakin tulu. Idan aka taba su dole jama’a su girgiza, idan kuma aka bar su kasar za ta cigaba da cutuwa. Irin wannan bumburutun ana kiransa ‘Informal Cross-Border Trade (ICBT)’.

Na uku shi ne cin amanar da makwabtan kasa ke yi mata wajen mayar da ita tamkar mazurarin zuke tattalin arzikinta zuwa wajensu. A duniya kaf, kasashe uku ne suka fi fama da matsalar miyagun makwabta. Na farko Amerika tana fama da matsalar shigar da miyagun kwayoyi ta Mexico. Sai Rasha wadda ke fama da Ukraine inda ake zuke mata iskar gas. Sai kuma Nijeriya wadda kasar Benin ta mayar bola inda take karbar kowanne tarkace tana karbar haraji sannan ta sake wa kayan fasali ta bari a shigar da su Nijeriya ta barauniyar hanya. Da haka suke yin arziki har suke biyan ma’aikata da sauran mawalati. Yaushe rabon da ka ji an ce kwatakwalli sun shigo kasar nan Ci-rani?

To da a ce kowa zai yi aiki bilhakki, gwamnati da saukaka hanyoyi fitar da kaya. A yi noma ba kama hannun yaro, yan kasuwa su daina boye kaya, talakawa su biya haraji, mahukunta su daina cin hanci. Ina tabbatar muku idan aka tabbata a haka, boda za ta iya kasancewa shekara biyu a rufe ba tare da an galabaita ba.

Ta yiwu nan gaba kadan a daina tunanin wata aba shinkafa a koma kan sumogal din wasu abubuwan. Don haka kula da boda bai ta’allaka da nau’in kaya iri guda ba. Duk wani abu ake iya shigo da shi mahangurba ne ga tattalin arzikin kasa. Misali, a baya can sumogal din taki ake yi. Aka bar wannan aka koma na barasa da taba sigari. Aka daina aka koma gwanjo da motoci yanzu kuma ana yin na shinkafa. Ta yiwu idan ta bunkasa a kasa a koma fasa kwaurin wani abin kuma. Wajibi ne gwamnati ta yi da gaske ko kuwa a yi haihuwar guzuma.

%d bloggers like this: