AN KARRAMA MARUBUCI NAZIR ADAM SALIH

Sashen Koyar Da Hausa na Kwalejin Shari’a Da Addinin Musulunci ta makarantar Malam Aminu Kano da ke Kano, sun karrama Nazir Adam Salih saboda gudunmawarsa wajen habaka harshe da adabin Hausa.

Nazir yana cikin fitattun marubuta da suka daɗe suna bai wa harshen Hausa gudunmawa wajen habaka shi.
Ya rubuta tarin littattafan Hausa ababen koyi, dq kuma fina-finan Hausa, wasu daga cikin littattafansa sun haɗar da:-

-Kibiyar Ajali
-Alaƙaƙai
-Hindu
-Iska Mai Kaɗa Ruwa
-Zayyana
-Bindigar Kwali
-Damisar Takarda
-Kisan Boko
Da sauransu, Allah ya ƙara basira, amin.

Kabiru Yusuf Fagge

%d bloggers like this: