Yadda Rikici Ya Tarwatsa Zaben Kungiyar ANA

  • Home
  • Labarai
  • Yadda Rikici Ya Tarwatsa Zaben Kungiyar ANA

Yadda Rikici Ya Tarwatsa Zaben Kungiyar ANA

Daga Yaseer Kallah

A jiya Asabar, 2 ga watan Nuwamba, 2019 ne kungiyar marubuta ta kasa, ANA, ta yi shirin gabatar da zaben sabbin shugabanninta na kasa a jihar Enugu. Zaben sabbin shugabannin na daya daga cikin jerin shirye-shiryen da take gabatarwa a gurin taronta na shekara-shekara da ke daukar tsawon kwanaki uku tana gabatar da shi.

Kungiyar ta soma gabatar da taron marubutan a ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba, 2019, kuma taron ya samu halartar tarin marubuta daga kusan dukkan jihohin Nijeriya. Yawan marubutan da suka raja’a a jihar Enugu bai rasa nasaba ba da kasancewar wannan shekarar a matsayin ta zaben sabbin shugabanni.

‘Yan takara hudu ne suka nuna sha’awar tsayawa shugabancin kungiyar. Akwai Barrister Ahmad Maiwada, wanda ya fito daga reshen birnin tarayya, Abuja; Camillus Ukah, mataimakin shugaban kungiyar ta kasa kuma dan reshen jihar Imo; Dokta Ofonime Inyang, sakataren kungiyar kuma dan reshen jihar Akwa Ibom; sai kuma Chike Ofili, wanda ya fito daga jihar Ikko.

Taron ya zo wa marubutan da suka halarce shi da bazata ta hanyar gaza samun kyakkyawan shiri kamar yadda aka saba gabatarwa a baya. An ji da yawa daga cikinsu suna kukuni da ‘yan gunaguni, wasu har suma Allah-wadai da gwamnatin da ke shirin barin gado ta Malam Denja Abdullahi. Da yawansu sun koka a kan abubuwa da dama, kamar matsalar masauki, wanda a baya kungiyar ce ke da alhakin nema wa marubutan masauki da kawo motocin da za su dinga jigilarsu daga masauki zuwa guraren taro, amma a yanzu suka janye jikinsu tare da daura dukkan alhakin a kan marubutan. Bayan wannan akwai matsalar fara taro a kan lokaci; gaza ciyar da marubutan a gurin taron; soke yawon bude ido da ziyarce-ziyarce guraren tarihin jihar; rashin halartar wasu manyan mutane da kungiyar tai ta yayata cewar za su halarci taron da dai sauran matsaloli da dama da tun ma kafin a zo zaben, marubuta da dama suka ayyana taron a matsayin mafi muni da kungiyar ta taba gabatarwa.

Lokacin kada kuri’ar ya zo a daidai lokacin da marubutan suka gama hasala har ma wasunsu na zargin ko gwamnati mai shirin barin gado na shirya wata manakisa ta tafka magudi domin tabbatar da cewa mataimakin shugaban kungiyar, Camillus Uka, kuma zabin shugaba mai shirin barin gado, Denja Abdullahi, ne ya lashe zaben.

Rikici ya soma tashi a lokacin da ake gabatar da babban taron tattaunawar kungiyar na shekara-shekara (AGM). A lokacin wasu magoya bayan wasu ‘yan takarkaru sun gama amanna da cewa akwai wata boyayyar manakisa da gwamnati mai shirin barin gado take shiryawa domin kada ‘yan takararsu. A ka’idar kungiyar, duk lokacin zabe mambobi ne ke zabar kwamitin da za su gudanar da zaben, sannan sai su shuwagabannin kungiyar su bayar da shawarar sunan wanda zai jagoranci kwamitin. Sabanin haka, sai Denja Abdullahi ya mike ya bayyana cewa su ne za su kafa wannan kwamitin gudanar da zaben. Hakan ya harzuka sauran ‘yan takarar inda suka ce atafau ba su yarda ba. An shirya hakan ne domin a yi masu magudi. Nan take dakin taron ya hargitse da rigima. Ran mutane da dama ya baci. Da kyar da gumin goshi wasu tsofaffin shuwagabannin kungiyar kamar Odia Ofeimun, Farfesa Remi Raji da Dokta Wale Okediran suka shawo kan marubutan ta hanyar kiran ‘yan takarar da zaunawa da su domin a yi sulhu. Daga karshe suka amince a kan kowanne dan takara zai bayar da mutum daya da zai zamo wakilinsa a cikin kwamitin gudanar da zaben. Hakan ya yi tasiri gurun yayyafa wa zukatan fusatattun marubutan ruwan sanyi. Daga karshe kowanne dan takara ya bayyana sunan wanda zai wakilce shi. Hakan ya sa Denja Abdullahi ya kara mikewa ya bayyana dokokin zaben. A jawabinsa, ya bayyana cewa duk wanda zuwansa na farko kenan ba zai yi zabe ba, ko da kuwa ya yi rijistar zuwa taron. Bayan su sai daliban makarantar firamare, sakandare, da ‘yan jami’ar da ba su kammala digiri ba. Dukkansu za su zauna kawai su zuba ido a kan yadda za a gudanar da zaben.

Bayan kammala gabatar da wakilan ‘yan takara da su zamo kwamitin gudanar da zabe sai aka ce kowa ya fita waje domin tantance masu shirin kada kuri’a. Kowa ya fita waje aka yi dafifi a bakin kofar dakin taron. Daya daga cikin jami’an gudanar da zaben ta dau lasifika ta fara sanar da cewa a hannunsu akwai jerin sunayen mutanen da suka cancanci su yi zabe. Ma’ana mutanen da suka cika sharuddan zabe da aka lissafa a baya. Daga nan ta soma kiran sunayen daya bayan daya; jiha bayan jiha.

A nan ne komai ya dagule. Domin kuwa sunayen kusan kashi daya bisa uku na mutanen da ke ganin sun cancanci su jefa kuri’a ya yi batan dabo a takardar. Misali, wakilan jihar Kano 17 ne suka halarci taron, kuma dukkansu sun cika sharudan yin zaben amma sai aka kira sunayen mutane 7 kacal aka ce su suka cancanci yi zaben. A gaskiyance kuma, gaba daya sauran goman sun cancanta domin har ma akwai irin su Kabiru Yusuf Anka da Aminu Salisu Giginyu da suka halarci taron sama da sau biyar. Jihar Katsina kuwa wakilai 19 ne suka je amma sai aka ce Dokta Abu Sabe ne kawai zai yi zabe. Abin ma da ya fi bai wa Katsinawan mamaki shi ne kin saka sunan Danmusa a cikin masu zabe duk kuwa da kasancewarsa daya daga cikin shugabannin kungiyar ta kasa masu shirin barin gado; dan takarar wata kujera a yanzu kuma wanda ya shafe kusan shekaru 7 bai yi fashin halartar taron ba.

Nan fa mutane suka harzuka. Masu zargi suka gazgata zarginsu na an shirya wata kutungwila ta rage yawan magoya bayan ‘yan takararsu domin bai wa wani dan takara damar hayewa cikin sauki. Hakan ya sa suka ce sam-sam ba za ta sabu ba. Ya za su taho daga wata uwa-duniya domin gabatar da zabe sannan a hana su duk kuwa da cewa sun cika dukkan sharuddan da aka gindaya na zaben.

Abin mamaki, ashe akwai da yawa daga cikin masoyan Ofonime Inyang, sakataran kungiyar mai shirin barin gado da ya balle ya ce shi ma takara zai yi duk kuwa da shugaba Denja Abdullahi ya tsayar da mataimakinsa Camillus Ukah takarar kujerar, da su ma aka haramta wa yin zaben. Hakan ya sa ya tunzura, ransa ya yi matukar baci.

Inyang ya zaburo ya banke tsohon shugaban kungiya, Odiah, yana wasu harbe-harbe, ifface-ifface tare da fadar bakaken maganganu a kan Denja da kuma cewa jami’an tsaron da ke gurin cewa su harbe shi din. Ya dinga damko magoya bayansa yana turo su cikin dakin taron tare da fadin dole sai sun yi zabe. “Ina Denja din?” Ya dinga fada. Nan fa suma sauran na waje da aka haramta wa zabe suka danno suka shigo. Dama sun gama hasala. Wayon da aka masu na cewar akwai wani jerin sunayen da za a kara kira ne ya sa suka jira. Ashe dai duk labari ne. Dakin taro ya hautsine da hargowa da rikici. Ga dare ya yi; ga kuma ba wutar lantarki. Shugabannin zabe suka iya yinsu amma abu ya ki lafawa. Har yana nema ya koma abin da ba a so ji ba.

Rikicin da Inyang ya yi sai kuma ya bai wa mutane mamaki. Yaushe kana sakataran kungiya amma a fitar da jerin sunayen masu zabe amma ba da saninka ba. Ashe dai shugaba Denja ne shi kadai ya ja kofa ya datse; ya dau takarda ya rubuta sunayen da yake so ba tare da sanin sauran shugabannin kungiya, ciki har da sakatarensa Inyang.

A ka’ida, jerin sunayen dukkan wani wanda ya taba halartar taron kungiya na kasa, tun daga na farko har zuwa shekarar da ta gabata, za a dauko a zo da shi taron. Duk wanda ya zo a duba. In da sunansa ya shiga. Amma sam ba a yi haka ba. Shugaban kungiya ne kawai ya san yadda ya zana sunayen. Su ma sauran shugabannin sai a dakin zabe suka yi tozali da sunayen.

Hakan ya sa suka kuma tabbatar da cewa Denja ya yi amfani da iko da mulkin mallaka gurin kassara yawan magoya bayan ‘yan adawan dan takararsa ta hanyar hana su zabe da sunan ba su cancanta ba. Abin mamaki har sakatarensa bai sha ba. Marubutan sun yi zargin an masa hakan ne saboda ya gaza yin biyayya, ya ce shi ma sai ya gwabza da dan takararsa Camillus. A cewar Denja Abdullahi, ‘yan takarar sun hayo wasu mutane da daga jihohi domin su zo su tara masu kuru’u. Hakan kuma ba zai taba sabuwa a ANA ba. Kila shi ya sa cikin mutane 19 na jihar Katsina, mutum daya ne aka yardarwa yai zabe. A dayan bangaren kuma da yawa daga jihar Imo suka samu damar shigewa.

Guri dai ya yamutse, wutar rikici ta ruru. Dole su Farfesa Remi Raji da Odia Ofeimun, suka nemi zaman minti 20 da ‘yan takarar domin a yi maslaha. Bayan sun zauna aka bai wa kowanne dama ya yi magana cikin minti biyar. A nan dai ta tabbata cewa shugaba Denja ne kawai ya bugi kirji ya rubuto sunayen wadanda yake son su yi zabe ba tare da sanin kowa daga cikin sauran shugabannin kungiyar ba.

Daga karshe Farfesa ya gayyato mashawarci ta bangaren shari’a na tawagar shugabanni masu shirin barin gado kan ya fito ya bayar da shawara ta fuskar shari’a game da yadda za a magance matsalar. Lauyan ya fito ya karanto wasu sashe-sashe daga kundin tsarin mulkin kungiyar da suka nuna cewa matukar irin haka ta faru dole a dage zaben.

Hakan kuma aka yi. Taro ya watse inda aka nausa wani otel domin walima. Bayan kammalawa aka yi sanarwar za a sanar da ranar zabe bayan kwamitin bayar da shawara sun zauna. Za kuma a yi zaben a kasa da watanni shida.

%d bloggers like this: