Jami’ar Dutsin-ma Na Cikin Halin Ha’ula’i – Kungiya Samar Da Zaman Lafiya

  • Home
  • Labarai
  • Jami’ar Dutsin-ma Na Cikin Halin Ha’ula’i – Kungiya Samar Da Zaman Lafiya

Jami’ar Dutsin-ma Na Cikin Halin Ha’ula’i – Kungiya Samar Da Zaman Lafiya

Daga Yaseer Kallah

Wata kungiya mai rajin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin Dutisin-ma mai suna ‘The Dutsin-ma United for Peace and Stability Association’ ta baiyana cewa jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-ma, jihar Katsina, na fuskantar rushewa matukar gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba gurin shawo kan matsalar da ke addabar jami’ar.

Shugaban kungiyar, Sufyanu Adamu, ya yi zargin cewa akwai wani yunkuri na rushe jami’ar da wasu mara sa gaskiya daga ciki da wajen jami’ar ke yi.

A dangane da jawabinsa, sam jami’ar ba ta gudanar da ayyukanta kamar yadda sauran jam’o’i ‘yan uwanta ke yi biyo bayan yadda ake karya ka’idoji da dokokin jami’ar.

A yanzu diban ma’aikata ya koma hannun masu cuwa-cuwar samar da aiki a cikin jami’ar. Jami’ar, ba tare da la’akari ba, na diban dalibai masu tarin yawa da yawansu ya zarce yawan da za ta iya dauka, sannan kuma da amincewar hukumar jami’ar,” Adamu ya fada.

Ya bayyana cewa babban abin da ya fi damun kungiyar shi ne halin ko-in-kula da ma’aikatar ilimi ke nunawa a kan abubuwan da ke wakana a jami’ar.

Duba da haka ne ya sa muke rokar gwamnan jihar, Aminu Masari, da mukaddashin shugaban jami’ar, Umar Dandani, da su magance matsalolin da ke addabar jami’ar ta hanyar kawo sauyi a jami’ar domin samun karatu da ayyuka masu inganci.

Da Daily Trust ta tuntube shi, kakakin jami’ar, Habibu Matazu, ya nemi kungiyar da ta gabatar da jawaban nasu ga sabon mukaddashin shugaban jami’ar.

%d bloggers like this: