ZUWA GA WAKILAN MARUBUTA A INUGU

Da fatan kun sauka jami’ar Godifire Okoye lafiya kuma an fara taro lafiya. Ina da yakinin cewa yanzu kun huta da gajiyar hanya da kuka sha, musamman wakilan jihar Kano da suka gamu da tutsun abin hawa har ta kai su ga kwanan daji. Wannan ma labari ne abin rubutawa.

Bayan haka, sanin kanku ne kuna wakiltar dubunnan marubuta da ke barbaje a sassan jihohin kasar nan wadanda mabanbantan uzururruka suka hana su zuwa wannan katafaren taro. To don haka, wajibinku ne ku aiwatar da abin da ya kai ku, watau zaben shugabannin da za su ja ragamar wannan kungiya har zuwa shekaru biyu masu zuwa. A wannan tsakani muna sa ran kungiyar ta bunkasa, sunanta ya kara yin kauri a tsakanin kungiyoyin kwararru na Afrika da duniya baki daya.

Kungiyar marubuta ta kasa wadda a turanci ake kira ANA a takaice, ita ce babbar rumfar marubuta na kowacce fuska. Don haka ma take kunshe da hazikan mutane daga kowanne janibin rayuwa. Kenan raya wannan kungiya ba adabi kadai aka raya ba, duniyar gaba daya aka raya. Domin babu abin da zai bunkasa idan ba tare da rubutu ba.

Kungiyar ta samu tagomashi da martaba tun daga kokarin shugabannin ta farko watau su marigayi Janar Mamman Vatsa da su marigayi Chinua Achebe da sauransu.
To amma duk da wannan martaba da madogara da kungiyar ke da shi, saura kiris su tafi a tutar babu, ganin yadda ake mata kanshin mutuwa da hawan kawara da nuna fifiko ba tare da jan kowa a tafi gaba daya ba. Wannan kuwa ya samo asali daga irin shugabannin da ake zaba ko ake turawa wakilci daga sassan jihohi.

Da alama zaben bana kan mage ya waye, marubuta sun fadaka. Gaba daya an ajiye bambace – bambancen da ke tsakani saboda ra’ayi na siyasa ko manufa ko madogara. Yanzu kowanne marubuci babban burinsa a tabbatar an zabi nagartattu kuma hazikan shugabanni da za su tabbatar da mafarkin magabatan kungiyar ya cika bisa ingancin hasashe. Babu kuwa wanda zai yi tsayuwar gwamen jaki dangane da haka sai ku wakilanmu.

Muna fata ku yi aniya, ku zabo mana fitattu, nagartattu, kuma jajirtattun shugabannin da za su kai mu tudun mun tsira. Wakilan arewa, kada ku bada mu. Ku hada kanku kamar tsintsiya a wannan wajen, na tabbata duk wanda kuka zaba shi ne zai ci zabe. Ku tuna cewar kuri’arku ita ce ‘yancinku.

A karshe, ina fata a kammala zabe cif-cif ba tare da inkonkilusif ba. Zaben inkonkilusif bai kamaci hamshakiyar kungiya kamar ANA ba.

Muna muku fatan alheri, da fatan za ku rika tsakuro mana wainar da za a toya a daidai lokacin zaben.

Allah ya sa ku zabo nagari. Ya dawo da ku gida lafiya.

Wassalam
Naku

Danladi Haruna
Sakataren Kudi na Kungiyar ANA reshen jihar Kano.

%d bloggers like this: