MTN ta dakatar da sabon tsarin cajin kudade

  • Home
  • Labarai
  • MTN ta dakatar da sabon tsarin cajin kudade

Kamfanin MTN na Nijeriya ya sanar da dakatar da sabon tsarin da ya fito da shi na yankar Naira 4 a dukkan sakanni 20 da aka yi yayin amfani da lambobin banki.

Wannan kuwa ya biyo bayan korafin da jama’a suka yi kuma kamfanin ya tuntubi masu ruwa da tsaki kan wannan batu.

Tun farko dai MTN sun tura wa masu mu’amala da su sakonnin cewar sun samu sahalewa daga bankunansu domin aiwatar da wannan tsarin. Sai dai bankunan sun ki yarda su amsa wannan ikrari inda da dama suka nuna rashin gamsuwar su kan wannan mataki.

A sanarwar da kamfanin MTN ya fitar, ya bayyana cewar, an dakatar da wannan tsari har sai abin da hali ya yi.

%d bloggers like this: