Zanga-Zangar Mace Daya Ta Janyo An Dakatar Da Malamin Wata Jami’a

  • Home
  • Labarai
  • Zanga-Zangar Mace Daya Ta Janyo An Dakatar Da Malamin Wata Jami’a

Zanga-Zangar Mace Daya Ta Janyo An Dakatar Da Lakcara

Daga Yaseer Kallah

Hukumar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta dakatar da daya daga cikin malamanta mai suna A. B Umar sakamakon zarginsa da laifin neman lalata da wata daliba kafin ta haye darasin da yake koyarwa.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Ashafa, ya bayyana hakan ga gidan talabijin din Channels a ranar Alhamis.

Ya ce an dakatar da malamin sakamakon wata zanga-zangar mutum daya rak da wata tsohuwar dalibar jami’ar Ahmadu Bello ta yi a jami’ar inda ta zargi Umar da laifin neman lalata da ita a shekarar 2013.

Dalibar, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta bayyana cewa malamin, wanda jami’ar Ahmadu Bello ta kora sakamakon laifin lalata da dalibai sannan daga baya jami’ar KASU ta dauke shi aiki, bai cancanci ya koyar a kowacce makaranta ba.

Mataimakin shugaban jami’ar wanda ya kasance shugaban kwamitin da aka kafa a cikin watan Oktoba domin ya binciki zargin da ake wa malamin ya bayyana cewa bai kyautu KASU ta kara daukar Umar aiki ba sakamakon abubuwan da suka sa ABU ta kore shi.

Ya ce sam jami’ar ba za ta amince da dukkan ire-iren ayyukan badalar nan ba.

Daga bisani ya kara da fadin cewa za su ci gaba da bincike a kan zargin da aka yi a kan malamin domin su tabbatar da cewa an gabatar da adalci.

A nashi bangaren, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yi Allah-wadai da abin da malamin ya yi na neman lalata da dalibar domin maki.

Ya kara da fadin cewa dakatar da malamin shi ne mataki na farko. Sannan za a gabatar da kwakkwaran bincike a kan malamin da ma wasu guda 15 da jami’ar Ahmadu Bello ta kora a kan laifin lalata da dalibai domin gabatar da su a gaban kuliya.

%d bloggers like this: