Rundunar Soji Ta Cafke Mayakan Boko Haram 16 Da Manyan Kwamandoji Biyu

  • Home
  • Labarai
  • Rundunar Soji Ta Cafke Mayakan Boko Haram 16 Da Manyan Kwamandoji Biyu

Rundunar Soji Ta Cafke Mayakan Boko Haram 16 Da Manyan Kwamandoji Biyu

Daga Yaseer Kallah

Rundunar sojin Nijeriya ta baiyana cewa ta kaddamar da wasu hare-hare a kan mayakan Boko Haram da ke labe a garin Pulka, karamar hukumar Gwoza, jihar Borno a ranar 20 ga watan Oktoba, 2019.

A cikin wani jawabi, jami’in watsa labaran rundunar sojin Nijeriya, Kanal Aminu Iliyasu, ya bayyana cewa sakamakon aikin, sun samu nasarar damke mayakan kungiyar guda 16.

Ya kara da fadin cewa bincike ya nuna cewa wasu daga cikin mayakan da aka kama din na daga cikin mayakan da suka kaddamar da farmaki a Pulka da Gwoza, ciki har da hallaka wasu jami’an ‘yan sandan Nijeriya a kwanakin baya.

Iliyasu ya ce biyu daga cikin ‘yan Boko Haram din na daga cikin jerin sunayen ‘yan Boko Haram da rundunar Sojin ta wallafa sunayensu inda take nemansu ruwa-a-jallo. Lambobinsu a jerin sunayen sune 41 da 90.

Ya ce su ne: Lawan Abubakar Umar Garliga da Bayaga Manye (wadanda ke kan lamba ta 41 da 90 a kan jerin sunayen ‘yan Boko Haram din da rundunar sojin ke nema ruwa-a-jallo).

Sauran ‘yan ta’addan da aka kama sun ne: Alhaji Umaru (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram), Goni Agwala (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram), Momodu Shetene (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram da kuma gyaran keke), Hassan Audu (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram), Usman Manye inkiya, Yega (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram), Ali Lawan (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram) da Modu Mallum (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram).

Sauran su ne: Modu Abubakar Jugudum, Bulama Ali, Umar Usman, Mustapha Alhaji Mele (mai samar da kayan aiki ga mayakan Boko Haram da kuma), Abor Lassan, Mallum Ari da Mala Bala.

%d bloggers like this: