Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Ba Mu Kafa Kwamitin Da Zai Yi Bincike A Kan Satar Yaran Kano Ba – Ganduje

  • Home
  • Labarai
  • Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Ba Mu Kafa Kwamitin Da Zai Yi Bincike A Kan Satar Yaran Kano Ba – Ganduje

Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Ba Mu Kafa Kwamitin Da Zai Yi Bincike A Kan Satar Yaran Kano Ba – Ganduje

Daga Yaseer Kallah

Gwannan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatinsa ba ta kafa kwakkwaran kwamitin da zai yi bincike a kan satar yaran jihar Kano guda tara da wasu ‘yan kabilar Igbo guda shida suka yi ba. ‘Yan kabilar Igbon sun fada da bakinsu cewa sun saci yaran tare da sauya masu suna da addininsu na Musulunci zuwa Kiristanci.

A kwanakin baya ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tserar da yara kanana guda tara da aka sace a jihar Kano tare da holin wasu ‘yan kabilar Igbo guda shida wadanda suka sheda cewar su suka sace yaran; suka canza masu suna da kuma tursasa su sauya addini zuwa Kitistanci kafin su sayar da su a garin Onitsha ta jihar Anambra.

A baya ne Gwamna Ganduje ya yi alkawarin zai kafa wani kwamiti da zai gabatar da bincike a kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta masu laifin.

Gwamnan, ta bakin sakataren yada labaransa, Malam Abba Anwar ya bayyana cewa kwamitin binciken zai yi nazarin abin tun daga tushe domin kare sake afkuwar irinsa.

Bayan nan ya sha alwashin cewa zai gayyaci iyayen yaran da aka kubutar din domin kara tattaunawa da kulla dangantaka.

Saidai kuma sati guda da fitar da jawabin, har yanzu gwamnan bai kafa wannan kwamitin da ya alkawarta ba.

Amma da yake tattaunawa da jaridar Kano Focus ta wayar ta salula, Malam Abba Anwar ya bayyana cewa gwamnatin tana kan aikin kafa kwamitin.

Anwar ya ce: “Kun san gwamnati tana bukatar ta laluba mutanen da za su iya jan ragamar kwamitin yadda ya kamata. Wannan shi ne abin da muke aiwatarwa yanzu.”

%d bloggers like this: