Karin Albashi: Shugabannin Kungiyar Kwadago na Jihohi za su soma tattaunawa da gwamnoni

  • Home
  • Labarai
  • Karin Albashi: Shugabannin Kungiyar Kwadago na Jihohi za su soma tattaunawa da gwamnoni

Bayan an samu maslaha tsakanin gwamnatin tarayya da hadaddiyar kungiyar kwadago kan batun karin albashi, a gobe Talata shugabannin kungiyar na jihohi za su hadu a Enugu domin tattauna yadda za su tunkari gwamnoni kan batun.

Manema labarai sun rawaito cewar an dauki kwanaki 182 tun bayan amincewar shugaba Buhari da karin mafi karancin albashi zuwa dubu 30 sannan aka yi yarjejeniyar da ta bayar da dama a yi kari ga manyan ma’aikata. Karin zai kasance akan 23.2% ga mataki na 7, sai 20% ga mataki na 8 mataki na 9 zai samu karin 19%; mataki na 10 zuwa na 14 kuwa an amince a yi musu kari zuwa 16%; sai kuma karin 14% ga manyan mukamai daga mataki na 15 zuwa na 17.

Ana ganin wasu jihohin za su iya aiwatar da wannan sabon albashi ba tare da tangarda ba domin kuwa tuni ma jihar Kaduna ta fara awon gaba. Wasu jihohin kuwa da alamu sai an kai ruwa rana.

%d bloggers like this: