Dalilin Da Ya Sa Gwamnati Da Jami’an Tsaro Ba Zasu Iya Kawo Karshen Boko Haram Ba – Sanata Kyari

  • Home
  • Labarai
  • Dalilin Da Ya Sa Gwamnati Da Jami’an Tsaro Ba Zasu Iya Kawo Karshen Boko Haram Ba – Sanata Kyari

Dalilin Da Ya Sa Gwamnati Da Jami’an Tsaro Ba Zasu Iya Kawo Karshen Boko Haram Ba – Sanata Kyari

Daga Yaseer Kallah

Kwamandojin soja na duba makamai da harsashan da suka kwace daga Hannun mayakan Boko Haram a shelkwatar bataliya ta 120 da ke Goniri, jihar Yobe

Sanatan da ke wakiltar Borno ta Arewa, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa ba za a iya hasashen karshen ta’addancin Boko Haram ba a Nijeriya har sai ita ma al’umma ta bayar da tata gudunmawar.

Sanata Kyari ya bayyana hakan a makarantar Barewa College, Zaria yayin taron ‘yan ajin 1979 na makarantar tare da bayar da kyautar girmamawa a cikin karshen mako.

Ya bayyana cewa bai wa yara tarbiya ta gari shi ne babbar abin da zai kawo karshen ta’addancin Boko Haram tare da hana samuwar ire-iren kungiyoyin ta’addancin.

Ya ce: “Idan na ce gwamnati da jami’an tsaro ba za su iya kawo karshen Boko Haram ba, ina nufin cewa akwai bukatuwar mu kara yin duba a kan yadda muke tarbiyantar da ‘ya’yanmu. Idan yaro ya taso da kyakkyawan tunani da hankali, babu wata akida da za ta canja masa tunani.

A yau shekaru 10 kenan muna yakar wannan ta’addancin, sannan kuma ba mu san lokacin da za mu dauka a gaba ba. Amma muna addu’ar ganin karshensa. Saboda haka, dukkanmu muna bukatar bayar da kyakkyawar gudunmawa domin samun nasara a kan ta’addancin.”

Daily Trust ta yi rahoton cewa Kyari na daya daga cikin tsoffin dalibai uku na makarantar da aka karrama a gurin taron.

Sauran su ne Justice Tukur Mu’azu na babbar kotun jihar Kaduna da Barrister Yakubu Bello Kirfi.

%d bloggers like this: