"BA NA TAUSAYINKI KO KADAN" MANSURAH ISAH

  • Home
  • Adabi
  • "BA NA TAUSAYINKI KO KADAN" MANSURAH ISAH

Fitacciyar tsohuwar jaruma, Mansurah Isah ta shiga cikin rikicin da ake bugawa tsakanin Sadiya Haruna da Isa A. Isa inda ta nuna bacin ranta da rashin sanin yakamata a cikin rigimar da ta barke. Ta bayyana haka a shafinta na Instagram:

“Subhana Subhana llah. Sadeeya bana tausayin ki ko kadan wallah, ban damu dake ba ko kadan, domin kin yankewa kanki rayuwar da kike so da halin da kike son ki tsinci kanki. Damuwata, kukana yaranki da wayenda zaki haifa a nan gaba da basu ma duniya a lokacin da kika wulakanta kanki.

Duk abinda mukayi yana nan a social media and it will stay sadiya. Even after u delete all your post, the damage has already been done. Banzan ce bazaki samu mijin aure ba, akwai masu imani. But just imagine your children in sunyi fada da mutane, zagin da zaayi musu na irin abinda mamansu ta aikata lokacin da take budurwa. Komu da bamuyi haka ba, film kawai mukayi muka fita lafia, ana zagin yaran mu ana kiran iyayen su suna, suna kuka kuma basu jin dadi. Balle ke. Nasan Allah ne mai shiryawa kuma zaki iya shiryuwa, but imagine the consequences on your family n children. Wallah wani lokacin dan yarana ina hakuri da abinda nake so kuma nasan bashi da alheri, dan yarana nakan kai zuciyata nesa dan siya musu musu mutunci a idon duniya. Ana cewa equality for all. But duk abinda mukayi a matsayin mu na mata wallah yana nunawa ajikin mu. Mufa ba yan america bane, we are blacks, we have culture, we have religion and we have manners. Inma ana zugaki ne, kice musu su tayaki yi bazaki yiba, kiga ko zasuyi. In kinyi abu mara kyau kuma Allah ya rufa miki asiri, to Allah yana sonki da rahama ne, sai ki cigaba da tuba, domin Allah baya son tozarta ki, amma Allah ya rufa miki asiri, kinyi abu a boye kuma Allah bai tona miki asiri ba, amma baki gode mishi ba, dole sai kin tonawa kanki asiri. Tam Allah ya baki saa. Amma ki guji duniya. After knowing all this things u did, who will want to associate himself with you? Knowing komin dadewa in mukayi fada zaki tonawa kawarki asiri? Re think about your life. Stop all this nonsense on social media. Go to YouTube and see all your videos. Hotunan nonon ki a waje, duk jikin ki a waje, duk wani abu da kika taba posting a page dinki yana YouTube , weather You delete them or not. Be wise and live in peace. Forget about been famous, nothing last for ever, zaa dawo a manta dake adaina yayinki komin dadewa, but what about your future generation?”

Tags:
%d bloggers like this: