Sarki Sanusi Ya Yaba Wa Ganduje Kan Shirin Mayar Da Ilimi Kyauta Kuma Dole

  • Home
  • Labarai
  • Sarki Sanusi Ya Yaba Wa Ganduje Kan Shirin Mayar Da Ilimi Kyauta Kuma Dole

Daga Yaseer Kallah

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan shirin mayar da Ilimi kyauta kuma dole a jihar Kano, duk da wutar rikicin da ta jima tana ruruwa a tsakaninsu.

Wani jawabi da kakakin gwamnan, Abba Anwar, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, ya bayyana cewa sarkin ya taya gwamnan murna tare da yaba masa kan yunkurin, inda ya ce, “Na amince da cewa wannan shiri ne na gaskiya domin kokarin hidima ga mutanen Kano da al’umma baki daya.”

Jawabin ya kuma yanko inda Sarki Sanusi yake cewa, “wannan shi ne ainahin abin da kasar nan take bukata. Muna bukatar sanya mahimmanci da jajircewa gurin tabbatar da hakan domin Ilimi shi ne kashin bayan kowacce al’umma.

“Abin da gwamnan yake yi abu ne na koyi, sahihi kuma wanda aka gabatar domin cigaban al’umma; wanda kuma ya kamata sauran jihohi su yi koyi da salon shugabancin mai girma gwamna.”

Sarkin ya bai wa dukkan sauran jihohin kasar nan shawara kan su yi koyi da wannan shirin.

Anwar ya bayyana cewa sarkin ya yi yabon a sa’ilin da gwamnan ya karbi tawagar bankin Zenith, karkashin jagorancin shugaban yankin Arewa maso yamma, Sani Yahaya, a gidan gwamnatin Kano.

Tags:
%d bloggers like this: