Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Jawabi Game Da Batun Auren Shugaba Buhari Da Sadiya

  • Home
  • Labarai
  • Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Jawabi Game Da Batun Auren Shugaba Buhari Da Sadiya

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Jawabi Game Da Batun Auren Shugaba Buhari Da Sadiya

Daga Yaseer Kallah

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin da ke kai-kawo na wai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na shirin kara mata.

Rahotannin sun bayyana cewa a yau ne za a daura auren shugaban kasar da ministar ayyukan agaji da kula da annoba, Sadiya Umar Farouk.

Rade-raden sun biyo bayan dadewar da mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi a kasar Saudi Arabia da Ingila ba tare da dawo gida ba.

A dangane da wata majiya da ta nemi kar a ambaci sunanta, Aisha Farouk tana da matukar kusanci da Shugaba Buhari sannan kuma ‘yan gaban goshinsa ma na matukar kaunarta.

The Nation ta yi rahoton cewa mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Femi Adesina, ya yi watsi da jita-jitar inda ya ce labarin kanzon kurege ne, kuma ya yi nesa da gaskiya.

Shugaba Buharin ya gabatar da sallar Juma’a a masallacin fadar shugaban kasar da ke Abuja. Mutanen da ya gabatar da sallar tare da su sun hada da hadimansa, wasu daga cikin ministoci, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da kuma Sanata Kabir Ibrahim Gaya.

%d bloggers like this: