JIMA'I DOMIN CIN JARRABAWA: AN FARA YI WA 'YAR JARIDAR BBC BARAZANA DA RAYUWA

  • Home
  • Labarai
  • JIMA'I DOMIN CIN JARRABAWA: AN FARA YI WA 'YAR JARIDAR BBC BARAZANA DA RAYUWA

JIMA’I DOMIN CIN JARRABAWA: AN FARA YI WA ‘YAR JARIDAR BBC BARAZANA DA RAYUWA.
‘Yar jaridar nan ta BBC, Kiki Mordi wanda ta yi binciken kwakwaf a kan yadda malaman jami’a ke amfani da damarsu gun cin zarafi da lalata da ‘yan mata ta fara karbar sakonni na barazana. Mordi ta bayyana cewa ta fara samun sakonni na barazana ne tun da rahoton binciken ya fita duniya.
‘Yar jaridar Kiki Mordi ta samu sha’awar yin wannan bincike kasancewar ita ma tana cikin wadanda abin ya taba shafa a baya, har ya tursasa ta ga barin jami’a, kafin ta kara samun damar komawa har ta kammala digirinta.
A yayin tattaunawa da jaridar Sahara Reporters, Mordi ta ce, “Na karbi sakonni na barazana tun da wannan aiki ya kammala, amma bana fargabar komai kasancewar BBC tana kula da tsaron ma’aikatanta.”
A cewarta kafin su fara wannan aiki sai da suka dukufa wajen addu’oi sosai domin kwantar da hankulansu da samun nutsuwa. Sannan ta halarci horarwa ba daya ba, ba biyu ba domin samun gogewa ta yadda aikin zai tafi kamar yadda ake so.
Ta bayyana cewa manufar wannan aiki shi ne a ji amonsa fiye da wanda za su maida martani, domin cin zarafi ta hanyar jima’i a bayyane yake. “Ina son abin ya yi kasa.” Ta ce.
Mordi ta bayyana farin cikinta na yadda abubuwa suka fara sauyawa tun daga bayyanar rahoton binciken. “Ina mai tabbatarka maka cewa Jami’ar Legas ta kori daya daga ciki malaman da aka kama yana cin zarafin daliba. Na tabbata abin ba a nan zai tsaya ba, har sai an dau hukunci. Dole mu kawar da dabi’ar nan ta yi wa masu laifi sulke.”

%d bloggers like this: