Kano Poly Za Ta Hukunta Malamin Da Ya Nemi Yin Lalata Da Daliba

  • Home
  • Labarai
  • Kano Poly Za Ta Hukunta Malamin Da Ya Nemi Yin Lalata Da Daliba

Daga Yaseer Kallah

Kwalejin fasaha ta jihar Kano, Kano State Polytechnic, ta kafa wani kwamiti domin ladabtar da wani malamin kwalejin mai suna Ali Shehu, wanda da bakinsa ya amsa laifin yunkurin lalata da wata daliba.

KANO POST ta yi rahoton cewa rundunar ‘yan sanda ta ci gaba da tsare Ali Shehu, malami a sashen ilimin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa na kwalejin, bayan ya amince da aikata laifin yunkurin lalata da wata daliba.

A yayin tattaunawa da jaridar KANO POST, shugaban kwalejin, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya bayyana cewa kwamitin zai kuma gabatar da bincike a kan wani malami mai suna Aminu Chedi da ake zargi da laifin karbar kudi daga hannun dalibai.

Daga karshe Kurawa ya yi kira ga daliban kwalejin da su gujewa dukkan wani mugun aiki da zai zubar wa da kwalejin mutunci a idon al’umma.

%d bloggers like this: