BUHARI YA JAGORANCI ZAMAN TARO NA MUSAMMAN

  • Home
  • Labarai
  • BUHARI YA JAGORANCI ZAMAN TARO NA MUSAMMAN

Buhari Ya Jagoranci Zaman Taro Na Musamman:
A yau Litinin shugaba Buhari ya jagoranci taro na musamman na shugabanni masu gafaka (Executive Council) a fadarsa dake Abuja. Taron ya biyo bayan sauke zaman da aka shirya za a yi a ranar Asabar.

Hukumar kula labarai ta Najeriya (NAN), ta labarto cewa an fara taron ne da misalin karfe 12:05 na rana, kuma ana sa ran zaman zai tattauna ne a kan batun kasafin kudin na shekara ta 2020.

Wadanda suka halarci zaman sun hada da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbanjo da Sakataren Gwamanatin Tarayya, Boss Mustapha.


Sannan akwai Abba Kyari da shugabar ma’aikata ta riko Folasade Yemi-Esun da kunshin ministoci. Ana sa ran ministan kula da jiragen sama, Sanata Hadi Sirika zai gabatar da jawabi na musamman a gurin.

%d bloggers like this: