AN RANGADAWA KUNGIYAR MALAMAN JAMI'A KISHIYA

  • Home
  • Labarai
  • AN RANGADAWA KUNGIYAR MALAMAN JAMI'A KISHIYA

An Rangadawa Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) Kishiya:
Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta samu kishiya biyo bayan samuwar wata sabuwar kungiyar mai suna Congress of University Academics (CONUA). Rahotanmu ya binciko cewa wasu mambobi na ASUU ne suka balle domin kafa wannan sabuwar kungiyar. Sun kuma bayyana cewa sun balle ne domin dawo da martaba gwagwarmayar da aka san malaman jami’a a kai ta samar da zaman lafiya a jami’oin Najeriya tare da samun cigaba. Shugaban tsare-tsare na sabuwar kungiyar na kasa, Niyi Ismaheel ya bayyana a taron kungiyar na farko da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jamiar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife cewa an kafa kungiyar ne domin Samar wata sabuwar hanyar tuntuba don warware matsalar da ta shafi walwalar mambobinsu tare da kawo karshen tasgado ga karatun dalibai yake shiga a duk lokacin da aka shiga yajin aiki.
Sabuwar kungiyar da aka assasa ta a jamiar OAU na da mambobi a Jamiar Ambrose Alli da Jamiar Tarayya ta Oye Ekiti da Jamiar Tarayya ta Lokoja da Jamiar Jiha ta Kwara sai kuma Jamiar Molete dake Illori.
Sai dai yayin tattaunawa da Ministan Kwadago Chris Ngige a jiya, ya tabbatar da cewa sabuwar kungiyar ba ta da rijista. Ya ce, “Har yanzu ba mu yi musu rijista ba, amma takardunsu na ma’aikatarmu, ba a kai ga duba su ba. Za mu duba, na sa kwamiti ya duba su.”

Tags:
%d bloggers like this: