An Sace Tokar Gawar Mahatma Gandhi

An Sace Tokar Gawar Mahatma Gandhi: A lokacin da Mahatma Gandhi yake cika shekaru dari da hamsin da haihuwa, a lokacin ne wasu suka shiga gidan tarihinsa suka sace wani bangare na tokar gawarsa, wanda ke ajiye tun shekarar 1948 a lokacin da aka kashe shi.
Shafin BBC sun rawaito yadda barayin suka rubuta “maci amana” da koren fenti a kan hotonsa.
Ita dai wannan toka an dauke ta ne a wani gini na tunawa da tsohon gwarzon, a yankin tsakiyar Indiya. Duk da cewa Gandhi mai tsattsauran ra’ayin Hindu ne, wasu mabiya addinin na Hindu na kalubalantarsa bisa tsarinsa na hadin kan addinan Hindu da na Musulunci. Ana zaton barayin na cikin masu wannan ra’ayi.
Amma jami’an tsaro na yan sanda a Rewa ta jihar Mahdhya Pradesh sun tabbatarwa ‘yan jarida cewa suna bincike akan satar.
Mai kula da inda tokar take Mangaldeep Tiwari yace, “Na bude kofar ginin Bhawan da sassafe, saboda bikin zagayewar ranar haihuwar Ghandi ce” Tiwari ya shaidawa shafin ‘The Wire’ na kasar Indiya.
“Da na dawo wajen karfe 11:00, na samu an sace tokar kuma an lalata hotonsa.”
Jami’an tsaro sun dukufa wajen gano wadannan bata gari. Yayin da masu ruwa da tsaki a kasar ta Indiya ke bada shawara da a kawo karshen irin wadannan matsaloli.
Gandhi dai ya jagoranci wata babbar gwagwarmaya ta lumana a kasar ta Indiya wadda ta yi nasarar kwato su daga mulkin mallaka na Birtaniya. Hakan yasa ya zama gwarzo ba ma a kasar ta Indiya ba, har a fadin duniya. A shekarar 1948 wani mai kishi da ra’ayin rikau na Hindu ya kashe shi ta amfani da bindiga. Saboda shahararsa ba a watsa tokarsa ba a kogi, sai aka raba ta a manyan guraren adana kayan tarihi har da Bapu Bhawan.

Tags:
%d bloggers like this: