Rikicin Hadiza Gabon Da Amina Amal: Kotu Za Ta Yanke Hukunci A Ranar 23 Ga Watan Oktoba

  • Home
  • Labarai
  • Rikicin Hadiza Gabon Da Amina Amal: Kotu Za Ta Yanke Hukunci A Ranar 23 Ga Watan Oktoba

Rikicin Hadiza Gabon Da Amina Amal: Kotu Za Ta Yanke Hukunci A Ranar 23 Ga Watan Oktoba

Amina Amal a harabar kotun tarayya ta jihar Kano

Justice Obiora A. Egwuatu na babbar kotun tarayya ta jihar Kano ya tsayar da ranar 23 ga watan Oktoba, 2019, a matsayin ranar da zai yanke hukuncin karar da ‘yar wasan fim din Hausa, Amina Muhammad Amal, ta shigar gaban kotun inda take zargin ‘yar uwar sana’arta Hadiza Aliyu Gabon da laifin ci mata zarafi da keta haddi.

Bayan nan kuma, a ranar kotun za ta yanke hukunci a kan kalubalen farko da lauyan Gabon ya shigar wa kotun inda yake kalubalantar huruminta na sauraron karar tare da yanke hukunci a kai.

Amal ta shigar da karar a kotun inda take bukatar Hadiza Gabon ta fito bainar jama’a ta ba ta hakuri tare da ba ta zunzurutun kudi har naira miliyan 50 a matsayin diyyar farmaki, azabtarwa da cin zarafin da ta mata.

Lauyan Gabon, Sadiq Sabo Turawa, ya kalubalanci hurumin kotun na saurarar karar, inda ya yi ikirarin cewa an aikata keta haddin dan adam din da ake zargin a gurin da ba ya cikin hurumin kotun. Ya ce ko da ma da gaske an aikata laifin, to ba a jihar Kano aka aikata ba.

Saidai kuma a nashi bangaren, lauyan da ke kare Amal, Faruq Umar, ya soki kalubalen lauyan Gabon, inda ya bayyana shi a matsayin kalubalen da bai cancanta ba kuma mara amfani.

%d bloggers like this: