KUNGIYAR KWADAGO TA YI BARAZANAR TAFIYA YAJIN AIKI

  • Home
  • Labarai
  • KUNGIYAR KWADAGO TA YI BARAZANAR TAFIYA YAJIN AIKI

Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Tafiya Yajin Aiki: A ranar laraba ne hadaddiyar kungiyar kwadago ta ma’aikata (NLC) ta yi barazanar tafiya yajin aiki na kasa a ranar 16 ga watan, Oktoba, 2019, matukar gwamnatin tarayya ta gaza kiran taro na kwamitin dake tuntuba da tsara yadda sabon albashi zai kasance.


Kungiyar kwadagon (NLC) da takwararta ta ‘yan kasuwa (TUC) a yayin ganawa da Hadaddiyar Hukumar Tuntuba Ta Ma’aikatar Gwamnati (JNPSNC) a Abuja ta bayyana cewa za ta iya tafiya yajin aikin idan aka gaza biya musu bukatansu.
Gwabnatin tarayya tare da hadaddiyar kungiyar kwadago sun gaza cimma matsaya bisa mafi karancin albashi, kusan wata shida da suka gabata.


A sanarwar da suka sa wa hannu, shugaban kungiyar kwadago Ayyuba Wabba da takwaransa Quadri Olaye (TUC) da shugaban riko na (JNPSNC), sun bayanna yadda kungiyoyinsu suka yi hakuri tare da bibiyar gwamnatin.


Sun bayyana yadda kungiyar kwadagon ta sauya ra’ayinta akan ainahin kudirinta na biyan kashi 66.6 cikin dari akan ma’aikatan dake matakin aiki na 7 zuwa 17, inda ta amince da biyan kashi 29 cikin dari daga ma’aikatan dake matakin aiki na 7 zuwan 14, sai kuma kashi 24 cikin dari ga ma’aikatan dake matakin aiki daga 15 zuwa 17.


Amma duk da irin wannan sadaukar da suka nuna, kungiyoyin sun ce gwamnatin ta kafe a cewa za ta biya kashi 11 cikin dari ga ma’aikatan dake matakin aiki na 7 zuwa 14, sannan kashi 6.5 cikin dari ga ma’aikatan dake matakin aiki na 15 zuwa 17.


Kungiyar kwadagon ta koka cewa darajar naira ta fadi daga naira 150 akan dala 1, a shekara ta 2011, zuwa naira 360 akan dala 1 a shekara 2019, wanda ke dauke da banbancin kashi 140 cikin dari.
‘Yan kwadagon sun bayyana cewa tun wannan lokaci mafi karancin albashi naira 18,000.00 wanda ya nuna irin wahalar rayuwa da ma’aikata suka shiga, saboda hauhawar da farashin kayan masarufi suka dinga yi.


Haka nan sun bayyana yadda farashin litar man fetur ya tashi daga naira 87 zuwa naira 145, wanda alkaluma ke nuna tashinsa da kashi 60 cikin dari. Hakazalika an samu karin kudin wuta har na kashi 60 cikin dari. Kungiyar kwadagon ta bayyana yadda kwanan nan gwamnatin ta tarayya ta aiyana karin haraji akan kayan da ake saya wato (Value Added Tax) daga kashi 5 cikin dari zuwa 7.2 cikin dari.


Kungiyar ta yi kira da a gaggauta kirawo taro na wannan kwamitin don warware abin da aka fara tun a 28 ga watan Mayu cikin sati guda. Shi dai kudiri na biyan mafi karancin albashi tun a 18 ga Afirilu shugaban kasa yasa masa hannu, amma har yanzu abin ya gagari Kundila.

Tags:
%d bloggers like this: