Da Dumi-Dumi: Kotu Za Ta Yanke Hukunci A Kan Shari'ar Ganduje Da Abba A Ranar Laraba

  • Home
  • Labarai
  • Da Dumi-Dumi: Kotu Za Ta Yanke Hukunci A Kan Shari'ar Ganduje Da Abba A Ranar Laraba

Da Dumi-Dumi: Kotu Za Ta Yanke Hukunci A Kan Shari’ar Ganduje Da Abba A Ranar Laraba

Kotun sauraren kararrakin zaben kujerar gwamnan jihar Kano ta tsayar da ranar Laraba, biyu ga watan Oktoba, 2019, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a kan karar da dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya shigar mata, inda yake kalubalantar bayyana sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da hukumar zabe ta kasa, INEC, ta yi a matsayin dan takarar da ya lashe zaben gwamnan da aka kada a ranar 9 ga watan Maris.

Sanarwar tsayar da ranar yanke hukuncin ta fito daga wani sakon tes da sakataren kotun ya tura wa jam’iyoyin da abin ya shafa.

%d bloggers like this: