DA SAURAN RINA A KABA: RIGIMAR GWAMNA GANDUJE DA SARKIN KANO SANUSI

  • Home
  • Labarai
  • DA SAURAN RINA A KABA: RIGIMAR GWAMNA GANDUJE DA SARKIN KANO SANUSI

Wata kungiya dake rajin dawo da martaba da kima ta jihar Kano da kwamared Ibrahim Waya ke jagoranta ta ce ta bankado wani sabon shiri da gwamnatin Kano take yi na sauyawa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II masarauta, daga Kano zuwa masarautar Bichi, wanda za ta maye gurbinsa da Sarkin Bichi Alh. Aminu Ado Bayero.

Kwamared Ibrahim ya yi Allah wadai da wannan yunkuri, kuma ya ce sun fasa kwai ne don ankarar da gwabnatin tarayya tare al’umma abin da ake ciki.

Wannan kungiya ta bayyana cewa har yanzu ba su san da zaman wasu masarautu a Kano ba, face masarautar Kano da Muhammadu Sanusi II ke mulka. A cewar Wayya, “tun da batun  yana gaban kotu, babu mai tursasu da amincewa da fadada masarautar.”

Kungiyar ta yi kira da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya janye kudirinsa saboda irin rashin kwanciyar hankalin da wannan yunkuri zai iya kawo jihar ta Kano. Kungiyar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da shugabannin siyasa da dattawan gari da masana tare da masu fada a ji da su isarwa da Gwamnan irin hadarin da ke cikin wannan yunkuri.

Hakazalika kungiyar ta yi barazanar kira ga gwamnatin tarayya da ta aiyana gwabnatin ta Se Ta Kwana a jihar Kano, matukar Gwamna Abdullahi Ganduje ya gabatar da wannan yunkuri da ake zargi, saboda kaucewa abin da kan iya faruwa.

Sai dai gwamnatin Kano ta bakin sakataren yada labaranta, Abba Anwar, ta musunta wannan labari da ta kira na kanzan kurege. Anwar ya fadawa kafofin yada labarai cewa shi ma ya tsinci wannan labari a gari, wanda bai san daga ina ya fito ba.

Wannan dai bai hana jama’a tofa albarkacin bakinsu akan wannan dangantaka ta gwamnati da masarauta da ta yi tsami. Abubuwan da ke faruwa na kokarin aika sako ga jama’a, musamman masu goyon bayan bangarorin biyu. A yan kwanakin da suka gabata an ga yadda aka saka hotuna sababbin sarakuna na Kano a bangon dakin taro na mika sandar mulki (Coronation Hall) wanda aka gina shi yayin ba wa Sarkin Muhammadu Sanusi II sanda a baya. Inda labarin yake shi ne yadda aka sa hoton Sarki Muhammadu Sanusi II a karshe wanda bai yi mutane dadi ba, ganin cewa an yi hakan da wata manufa. mutane����#

Tags:
%d bloggers like this: