WATA SABUWAR ZANGA-ZANGA TA BALLE A MISRA

A shekara 2011 Misirawa suka gudanar da zanga-zanga don kawo sauyi a kasar. A halin yanzu wata sabuwa ta balle, a yayin da mutane suka yi cikar kwari a Dandalin Alkhahira da wasu sassa na kasar na nuna rashin goyon bayansu ga gwabnatin Abdel Fattah Al-Sisi. Ga rahotannin da muka samu shi ne masu zanga-zangar na korafi na yadda cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a gwabnatin da Al-Sisi, ba tare da ganin wani yunkuri da zai magance matsalar ba.
An fara amfanin da shafikan sadarwa na Twitter wajen wannan yunkuri a Inda masu zanga-zangar suka dinga yada wasu kalamai irin “Jama’a na son hambarar da wannan shugabanci” da “Sisi ka saula daga mulki” da sauransu.

Akwai alamun cewa zanga-zangar za ta iya yin zafi, musamman idan an yi la’akari da yadda jami’an tsaro ke amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa jama’a. Shi dai Al-Sisi shi ne ya jagoranci sojojin Masar wajen hambarar da zababbiyar gwabnati ta fara hula ta farko a karkashin Muhammad Morsi a shekara ta 2013. Hakan yasa aka kargame shugaba Morsi, wanda ya rasu a cikin halin shariah a wannan shekara.

Dama dan gudun hijirar kasar Masar Mista Ali da ya samu mafaka a kasar Spain ya wallafa wani bidiyo a ranar Talata yana cewa idan har zuwa ranar Alhamis Al-Sisi bai sauka daga kan mulkin ba, ‘yan kasa za su fara zanga-zanga ranar a juma’a.

Gwabnatin Al-Sisi ta yi bakin jini musamman ta yadda ta zo, da irin rawarta wajen yin garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar. A watan Afirilu ne dai gwabnatin ta shirya zabe kan amincewa a yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, Inda ya bawa shugaba Al-Sisi damar zama shugaban kasa har
zuwa shekara ta 2030.

%d bloggers like this: