SARKIN KANO YA JINJINAWA BUHARI

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, CON ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kwamitin kwararru da ya samar don kula da harkokin arzikin kasa. Sarkin ya bayyanawa tashar BBC cewa duk cewa shugaba Buhari na da ministan kudi da shugaban babban banki, yana da bukatar irin wannan kwamiti. A cewarsa manyan shugabanni na duniya irinsu Donal Trump na Amurka na da irin wadannan kwamitoci. A bangaren wadanda aka dorawa wannan nauyi, Sarkin yace “mutane ne masu kwarewa a fannoninsu”.

Hakazalika Sarkin ya goyi bayan rufe kan iyakokin Najeriya da gwabnatin ta yi, domin abu ne da ya zama wajibi ta yi akokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasa. Ya bada misali da noman shinkafa, wanda idan ba a rufe iyakokin kasar ba, manoman ba su iya gogayya da shinkafa mai arha da za ta shigo ta barauniyar hanya ba cikin Najeriya.

Sarkin na Kano ya dada da cewa ” Kasashen da suke makwabtaka da Najeriya ba sa taimaka wajen kare tattalin arzikinta “. Wannan na daga cikin dalilan da yasa a baya mai martaba Sarkin suka dinga bada shawara a dau irin wannan mataki.

%d bloggers like this: