AN DAKATAR DA HARAJIN CBN

Majalisar wakilai ta Najeriya ta nemi babban bankin kasa (CBN) da ya dakatar da umarnin da ya bayar ga bankuna na su karbi kashi biyu (2) zuwa biyar (5) a cikin dari (100) na tsabar kudade da yan kasa suka shigar ko suka fitar a cikin asusun ajiya, matukar sun kai kimanin naira dubu dari biyar (500, 000.00) ga daidaikun mutane ko naira miliyan uku (3, 000,000.00) ga kamfanoni.

A zaman majalisar ne na ranar Alhamis 19 ga Satumba, 2019, wannan umarni ya fito. Sannan majalisar ta kafa kwamiti na musamman da zai yi nazari kan wannan yunkuri na babban bankin Najeriya, domin nazari da fito da mafita.

Tun daga bayyanar wannan umarni ne, mutanen Najeriya suka shiga kokawa kan wannan mataki da illarsa ga mutanen Najeriya a lokacin da ake cikin matsin rayuwa. Hakan ne ya ja hankalin majalisar na gaggawar daukar wannan mataki. Yanzu dai majalisar za ta saurari karbar rahoton wannan kwamiti kafin ta sanar da matsayinta.

Tags:
%d bloggers like this: