ABIN DA BABBA YA HANGO

ABINDA BABBA YA HANGO.

Yaro ko ya hau Rimi ba zai hango ba. Ina jin kun tuna da wannan Karin Maganar.

Iya fahimtata Baba Buhari ba zai rufe Iyakokin Kasa domin jin dadi ko kuma kawai son kuntatawa Talaka. Menene ribar.

Matsalar Shine muna da Gaggawa da saurin yanke hukunci da rashin hakuri. A shekarun da su ka wuce sai aka hana shigo da shinkafar waje. Nan da nan Mu ka fara Surutun an hana shinkafa shigowa mu kuma an bari ana fita da abincin mu. Yau sai aka rufe ba shiga ba fita, sai kuma mu ka fara surutun an rufe Iyaka an yiwa Talaka Kamshin Mutuwa.

Kowa ya zauna ya shantake,ma su Gonaki sun bazamo Birane yankan farce da wankin Takalma da Tallar kayayyaki a Kudancin Najeriya.
Idan an yi maganar noma sai su ce ina tallafi, Idan an bayar da tallafin su sayar su karo Aure. Sai ka rasa yadda za ka bullowa Talakan Najeriya. Wani abin Haushi da takaici gami da Dariya. Abinda ke bakunan Talakawa wai irin shinkafar da ake ci a Villa. Da ka yi maganar Shinkafa sai ka ji wani ya ce ai a Villa Yar waje ake ci. Sun ma kwafo wata Shinkafar Roba sun turo Facebook wai ita ake ci a Villa. 
Ana fara Maganar harajin VAT Talakawan Facebook su ka yi uwa da makarbiya wajen barnar Data kan Maganar VAT. Shi VAT haraji ne aksaran da bai shafi Gero,wake,Dawa,maiwa ko Masara ba. Mu talakawa me ya hada mu da shi. VAT haraji ne da ya fi tasiri a wuraren Shakatawa da Masaukan Baki Hotels da sauran kayan alatu. Shin ka ji Dangote ko Abdussamadu wadanda Ku ka fi sani sun yi korafi kan VAT ?

Maganar Cashless policy, tsarin takaita zirga zirgar kudi ma mun yi uwa da makarbiya duk da abin bai shafe mu ba. Ina mu ke da Dari biyar ko fiye da za mu kai Banki, kuma fa ana maganar Idan muamalar mu ka yi ta ta banki ba wai mu sanya tsurar kudi ba sisin mu ba zai yi ciwo ba. Misali na sayi gidan ka Miliyan Biyar na tura ma kudi ta Banki, babu wani Abu da zai taba kudi na ko na ka sai na transfer Wanda dama ana dauka.

Takaita zirga zirga ta kudi ba karamin rage matsalolin sace sace da fashi da damfara zai yi ba, amma abin mamaki yau hirar da ta cika Facebook kenan was su har da Zagi.
Idan Siyasa da Yan Siyasa ne takamar ka. Ka taba ji ko ganin Dan Kwankwaso ya fito ya na zage zage ko bata Data akan wani tsari na Gwamnati da bai ma sa ba. Ko ka taba Ganin Dan Mai Girma Sule Lamido ya na zage zage, kai da ganin Dan Sule Lamido sai dai a photo ya je aikin Hajji ko ya kammala Digiri na uku ko na biyu ko dai a wani waje Mai Daraja da Mutunci ya na Murmushi. A ina ka taba ganin Dan Baba Buhari na cacar Bakin kare Mahaifin sa. Sai kai da Idan ta dauro ba ka samun abinci sau uku? Da kudin Datar da za kai hasara gara ka sayawa mahaifiyar ka Geron da za tai Gasara da shi ko ‘Yar Tsala.
Idan takamar ka kare muradan ma su kudi. Ina ka taba ji ko ganin wani Ba’alashe ya fito ana rigima da shi kan haraji, ko ka taba jin wani Dan mai da akwai ya fito ya na zagin wani Gwabna ko wani mai mukami saboda an karawa Mahaifin sa haraji a yanayi ko harkar kasuwancin sa. Game da kulle Boda ka taba jin Dan Dahiru Mangal ko Shi Dahiru Malgal ya zagi wani ?

A lokacin da ‘Ya’yan wadannan ma’azurta da ma su Mulki da ‘Yan Siyasa su ka mayar da hankali wajen ganin sun sami ilmin da za su cigaba daga wajen da Mahaifan su su ka tsaya, kai kuma ka mayar da hankali wajen zage zagen cigaba da zama a cikin kangin talauci.

Duk wata mas’ala da ta zo ya kamata mu tsaya masana a bangaren su yi fidar abin ka fin mu fara tsoma baki, ba kawai daga kunna rediyo mun ji labarai sai mu fito Facebook mu fara aibata shugabanni. Da yawan mu ganin Najeriya mu ke kamar unguwannin da mu ka tashi, da yawa muna hukunta Najeriya da mulkin Najeriya a yadda mu ke ganin karkarar mu da kauyukan mu.

Mulkin Kasa kamar Najeriya ba abu ne na wasa ba da za mu yi sharhin sa a kwance ta waya a lungunan mu. A zuciyata ina da yakinin Rufe bodar nan zai zama alheri ga al’ummar Kasa. Abinda kuma ya ke a faifai Wanda kowa ya sani, kasashen da ke makwabtaka da mu sun fi mu cin Moriyar muamalar da mu ke da su, ba kuma kowacce Kasa ce ta damu da tsare mutuncin Najeriya ko kuma kula da kiyaye abinda zai cutar da Najeriya ba.

A kara hakuri a cigaba da addua tabbasa zuwa gaba kadan zaa fahimci amfanin Rufe Iyaka.

Auwal Danborno

%d bloggers like this: