Agent Raghav

An jima ana nuna finafinai irin su CSI, Cold Justice, Dexter, Brooklyn Nine-Nine, da sauransu. Sai dai gaba dayansu fim din Indiya na Agent Ragav ya fi tasiri. Ta yiwu saboda tagomashin fassarar Hausa da gidan talabijin na Arewa 24 ne ya jawo haka. Abin da ke burge mutane shi ne yadda tauraron ke amfani da kaifin basira da dogon nazarin bincike, wanda a karshe mai laifin sai ya je hannu.
To ashe mu ma anan Nijeriya muna da irin wannan hazikin jami’in binciken, wata DCP Abba Kyari. Babu shakka wannan zakakuri ya cancanci yabo da jinjina tare da kowanne irin fata ya samu nasara. Kasancewar sa a cikin hukumar yansanda ya saka da dama suka daina yi wa dakarun hukumar kudin goro wajen rashin tabuka komai.
Tsawon shekaru 19 da ya shafe cikin aikin dansanda, ya zuwa yanzu ya samu manya manyan nasarori da lambobin yabo. An ce sau uku a jere yana lashe lambar yabo ta gwarzon dansandan shekara a 2012, 2013 da 2014. Ya samu jinjina daga gwamnatin Legas da lambar yabo a matsayin gwarzon Afrika ta yamma duk shekara tun daga 2011 har zuwa 2017 da sauran lambobin yabo da dama.
Ba wai saboda iya saka kaki da fareti ya samu lambobin nan ba. Aiki ne da kwarewa da kums jajircewa ds kaifin ƙwaƙwalwa da rashin tsoro da rashin kasala da rashin cin hanci da rashin almundahana suka jawo masa wadannan martabobi.
Shi ne shugaban dakarun yansanda masu bincike da kai dauki (Intelligence Response Team) kuma memba ne Kungiyar Hafsoshin Yansanda ta Duniya (International Association of Chiefs of Police (IACP)) An ce wannan ƙungiya, ba kowanne dan dagajin dansanda ke shigar ta ba.
Nasarorin da ya samu na da yawa, amma ta baya bayan nan wadda ta sake fito da gaskiyar sa da jajircewarsa a zahiri ita ce, yadda suka iya sake cafke mugun mutumin nan na yankin Ibi da ke Jihar Taraba, watau alhaji Hamisu Wadume. Babu shakka wannan nasara ta wannan bawan Allah ya sa mun fahimci abubuwa da dama, daga ciki har da makasudin da har yanzu ba a kawo karshen hare – haren Boko Haram ba.
Muna addu’ar Allah ya taimaki DCP Abba Kyari Agent Ragav. Ya karya makiyansa kuma ya ba shi nasara kan dukkan manufofinsa na alheri.
Danladi Haruna
20th August 2019
%d bloggers like this: