Sultan Muhammad Alfatih – 1

TARIHIN SARKI MUHAMMADU ALFATIH DA YADDA YA KAWO KARSHEN DAULAR RUM

Wannan sarki shahararre ne a tarihin daular Usmaniyya. Jarumi ne mara tsoro wanda Allah ya bawa basira da kaifin hankali da hangen nesa. Kafin mu tsunduma bayanin yakin Kustantina, bari mu soma da tarihin sarkin a takaice da kuma tarihin garin na Kustantina. Daular Usmaniyyar da muke magana ita ce wadda Turkawa suka samar da ita karkashin sarkin Usman na daya, wani sarkin yaki ne daga askarawan Saljuk. Ya kafa ta a shekarar 1299 sannan ta zo karshe a shekarar 1922. Shekaru 623 kenan.

An haifi sarki Muhammad na biyu wanda ake wa lakabi da alfatih, watau mai nasara ranar 30 ga Maris 1430 miladiyya a birnin Edirne, wanda a wancan lokacin shine babbar shalkwatar daular Usmaniyya. Shi d’a ne ga sarki Murad na biyu, kuma shine sarki na bakwai a jerin sarakunan daular Usmaniyya. A yaren turkanci ana ambaton wannan suna Mehmet ko Mehmed ko Mahomet. An ce lokacin da aka haife shi mahaifinsa yana daki yana karanta suratul Fatahi aya ta karshe watau wadda ta fara da ‘Muhammadur rasulillahi…’ Lokacin da ‘yan bushara suka zo yana daidai inda ayar ake cewa, ‘li ya giza bi humul kuffar.’ Bai saurari mai bushara ba sai da ya kai karshe, sannan ya ji labarin cewa matarsa Uwargida Hauwa’u ta sauka lafiya, kuma ta samu d’a namiji. Ya mik’e cikin farin ciki ya tafi wajen mai jego, lokacin kuwa har an gyara jariri an sa masa kaya. Ya karbe shi ya yi masa huduba sannan ya ce, “albarkacin ayar da na karanta ta karshe na ambace shi da suna Muhammad.” Daga nan wasu ke ganin lallai sunan ya bi shi kuma albarkacin surar ma ta bi shi, shi yasa ake ambatonsa da Alfatih, ma’ana mai nasara. To amma bisa takamaiman zance ba a soma yi masa wannan lakabi ba sai da ya cinye birnin Kustantina, wanda hakan ya kawo karshen daular Rumawa mai shekaru fiye da dubu da kafuwa.

Ya soma karatun addini da na ilmi da wuri, domin an ce ya haddace alkur’ani mai girma yana da shekaru shida a duniya. Malam Gurani shi ya soma ba shi ilmin hadisi da na fikhu da na tauhidi. Daga nan babban malamin daular watau Sheikh Shamsuddini ya cigaba da koyar da shi fannonin ilmi dabam dabam. A lokacin da ya kai shekaru sha biyu a duniya, tuni ya haddace manyan littafan addini da na shari’a da na kere – kere da na likitanci. Saboda haka mahaifinsa ya sauka daga mulki ya bashi.

Saukar Sarki Murad na biyu ta jawo cece – kuce a ciki da wajen daular, a cikin gida dai manyan wazirai karkashin jagorancin Halil Pasha suka nuna adawarsu a fili, domin a ganinsu bai dace dan kankanin yaro ya jagoranci katafariyar daular da ke kewaye da makiya ba. A waje kuma Fafaroma na wancan lokaci da jin wannan labari ya zuga sarkin kasar Hungari ya warware amanar da ke tsakaninsa da musulmi, kuma ya yi shirin yakarsu.

Da sarki Muhammadu Mai nasara ya ga haka, sai ya nemi mahaifinsa ya dawo ya cigaba da mulkinsa, amma ya ki yarda da farko. Saboda haka sai d’an ya rubutawa mahaifinsa wasika a ciki ya rubuta cewa:

“Idan kai ne sarki to ka zo ka ceci jama’arka, idan kuma ni ne sarki, to na umarce ka ka zo ka jagoranci jama’ata. “

Da uban ya karanta wannan takarda sai ya ce, “d’a na ya d’aure ni da jijiyar jikina, babu abin da ya rage min face na aikata abin da yake buk’ata.” Nan da nan sarki Murad ya dawo karagar mulkinsa. Ya shirya yaki. Ya karya jama’ar Hungari, sannan ya tarwatsa mayakan kiristoci da suka zo domin rusa musulmi.

Tsawon lokacin da sarki Muhammad Mai nasara yana mulki shekara biyu, sannan ya dawo da sarauta ga mahaifinsa wanda ya shafe shekaru biyar yana mulki sannan ya mutu. Muhammadu Mai nasara ya dawo mulki karo na biyu yana da shekaru sha tara a duniya.

Dawowarsa ya dawo da k’ak’arfar niyya ta ruguza kafirai da ke masa gani – gani, domin an ce bayan saukarsa ta farko babu abin da ya mayar da hankali irin horon yaki da nazarin kai hari da harbi da sauransu. Su kuwa kafirai sai murna suke yi domin a ganinsu ta fadi gasassa musamman da suka ji cewa ya nad’a babban dan adawarsa a wancan lokacin watau Halil Pasha ya zama babban wazirinsa.

A cikin k’asa shekara d’aya sarki Muhammadu Mai nasara ya gina wata katuwar ganuwa a gefen teku wadda ta zama garkuwa ga jama’arsa kuma barazana ga kafirai musamman wajen wucewar jiragensu. Sarkin Kustantina, Sarki Falayologos ya bukaci a dakatar da wannan aiki, har ma yayi alkawarin zai biya dalar dinari miliyan uku domin a bar aikin. Da ya ga sarkin musulmi ya yi kememe, sai ya aiko masa da barazana amma duk da haka bai dace ba.

Sarki Muhammadu Mai nasara ya cinye birnin Kustantina yana da shekaru ashirin da daya a duniya, kuma shekaru biyu kacal da hawansa mulki a karo na biyu.


Za mu dora a mako mai zuwa.

%d bloggers like this: