Sarki Muhammadu Mai Nasara – 3

SARKI MUHAMMADU MAI NASARA …3

Sultan Muhammad Alfatih

SHIRIN YAKI
Kamar yadda muka fada a baya, sarki Muhammad mai nasara ya hau gadon mahaifinsa a karo na biyu lokacin yana da shekaru goma sha tara a duniya, wannan kuwa ya auku a shekarar 1451. A yadda tsarin yake, an hakikance yaro dan shekaru 19 kacal ba zai iya mulkin babbar daula ba ballantana har ya iya yunkuri kare ta ko fadada ta ba. Saboda haka shugabannin kiristoci ba su ga wata barazana tare da shi ba, sai suka soma shirin yadda za su murkushe daular Usmaniyya su shafe ta a doran k’asa.

Shi kuwa Sarki Muhammadu Mai nasara sai ya jawo manyan mutane jikinsa ya girmama su, kuma ya zamana tare da su a koyaushe. Tunaninsa da irin hangen nesansa ya wuce yadda aka yi tsammani. Cikin shekara guda da hawansa mulki, a shekarar 1452 ya gina babbar ganuwa wadda tun zamanin mulkin kakansa ake tunanin gina ta amma ba a cimma buri ba. Wannan gini ya tayar da hankalin daular Bazantiya, inda suka aiko wazirinsa takanas domin a dakatar da shirin, har ya yi masa alkawarin zai biya shi dinari miliyan uku. Da ya ki yarda sai kuma ya juyo da barazana ta hanyar yariman Ohana wanda yake tsare a birnin Kustantina. Amma shi Mai nasara bai razana bai fasa aniyarsa ba. Ya nada wani jarumi cikin sadaukansa wanda yake iya jera kwanaki barci dare da rana yana kula da aiki karkashin jagorancin Mahmud Fasha. Mun fada muku cewa Mahmud Fasha a da can bai so aka nada yaron sarki ba, har ma ya jagoranci adawar da ta sa ya sauka. Lokacin da ya dawo a karo na biyu kowa ya yi tsammanin kashe shi zai yi, to amma maimakon haka sai ya nada shi babban wazirinsa, kuma ya sanya shi kula da aikin wannan katafariyar ganuwa.

Haka nan Mai nasara ya aika da wasu amintattun mutanensa, karkashin jagorancin babban amininsa Ibrahim Khalil Fasha, suka tafi birnin Kustantina leken asiri. Suka shiga cikin tsakar dare lokacin a kwararon birnin babu kowa daga karnuka sai mashaya, sai masu gadi suna karakaina. Sarkin Bazantina ya bada umarnin duk wanda aka gani a waje da tsakar dare a kashe shi. Ibrahim da mutanensa suka yi amfani da kugiya suka haura cikin birnin, daya ya tsaya akan ganuwa ya tabe kwari da bakansa. Biyu suka tsirga ciki. Suna sauka sai ga askarawa masu gadi sun zo wucewa, nan take wanda ke saman katanga ya zabgawa na farko kibiya. Na biyun kuma Ibrahim ya gama da shi da takobi. Suka debi irin kasar da aka gina katangar birnin. Ita wannan katanga an yi mata wani irin gini na ban mamaki, an cakuda dalma da yumbu da wata irin kwalta wadda ruwa baya yi mata komai. Tsawonta ya kai kimanin kamu sittin, kaurinta kuwa kamu sha biyu ne. Sannan akwai kofofi daga sama inda ake iya harbin duk wanda aka ga dama daga nesa. Sannan suka auna fadin kwararon garin, suka auna zurfin kogin da ya kewaye birni Kustantina, sannan suka auna nisan gidan sarki daga bakin ganuwa. A karshe suka auna tsayin kurangar da ake hawa matattakalar. Suna komawa suka tarar Sarki Mai nasara na zaune yana jiran zuwansu. Nan da nan ya karbi bayanin da suka samo, zuba akan alkaluman lissafi. Bayan dogon nazari ya nuna musu irin niyyarsa. Ya ce, ” Za mu kera babbar bindiga wadda za ta iya ruguza kaurin katangar ta shige ciki.” Duk suka rike baki, domin kuwa a wannan lokacin babu bindiga irin wannan, kuma babu wata fasahar da za a iya kera irinta. Amma tuni Sarki Muhammadu Mai nasara ya zana irin bindigar da yake so a kera din.

Shi kuwa sarkin Kustantina, da ya hakikance babu makawa sai musulmi sun kawo masa hari, sai ya garzaya kasashen turawa neman taimako. Amma mun fada muku cewar akwai tsananin gaba tsakanin Rumawa yamma da na gabas, ga kuma gabar da ke tsakanin darikar kiristocin katolika da darikar Ogzados. Saboda haka Fafaroma Nikolas na biyar ya yi amfani da wannan dama ya ce muddin Bazantiyawa na bukatar taimako, to ya zama wajibi su amince da darikar katolika sannan su amince da wasu dokoki na musamman. Sarkin Kustantina ba shi da wani zabi face ya amince da dukkan sharadan. To amma hakan ya jawo daga talakawan birninsa. Aka yi ta zanga – zanga ana tofin alatsine ga wannan shiri. Shi kuwa ya yi amfani da karfi wajen tursasa jama’a, aka yi ta kashe mutane babu ji babu gani. Aka yi ta kama mutane ana daurewa a kurkuku. Daga cikin wadanda aka kama har da wani shahararren masanin kimiyya mai suna Orbanu, an ce dan asalin Jamus ne. Aka daure shi a kurkuku sannan aka garkama masa mari hannu da kafa. Wannan kisa da kame ya sa jama’a da yawa suka yi ta guduwa suna kaiwa Sarki Muhammadu Mai nasara caffa duk da kasancewar ba musulmi ba ne.


Bindigar Basiliska

Sarki Muhammadu ya samu labarin Orbanu, nan da nan ya tashi amintattunsa karkashin jagorancin Dorfanus suka haka rami mai tsawon gaske ta karkashin kasa tun daga bakin teku har zuwa cikin kurkukun suka dauko shi. An ce kafin a tsare Orbanus ya yi wa sarkin Kustantina tayin zai kera musu bindiga amma ya ki yarda ya kore shi. Daga samun tsiran kansa gaban sarki Muhammadu kuwa ya fadi bukatunsa; abubuwan da ake bukata wajen kera babbar bindigar ruwa. Nan da nan aka tattara masa dukkan abubuwan da ya nema. Ya kera wata bindiga da ya kira Basilika. Ita wannan bindigar tsawonta ya kai kamu ashirin da bakwai. Tana da nauyin kimanin kilo dari uku da hamsin. Kuma tana iya harba harsashi mai nauyin kilo 272 zuwa nisan kilomita uku. Shanu sittin ne suka jan wannan bindigar. Bayan wannan jibgegiyar bindigar an ci gaba da kera wasu matsakaita har guda saba’in.

%d bloggers like this: