SHARHIN LITTAFIN SADAUKI MAI DUNIYA – 2

  • Home
  • Adabi
  • SHARHIN LITTAFIN SADAUKI MAI DUNIYA – 2

Sarki Haruna kuwa ya na daure a can wani kurkukun karkashin kasa a kasar Damanga in da ya shafe shekaru cikin wahala da azabtarwa iri-iri, yayin da kuma Zubaida daya daga cikin matan da a ka tura Kwairanga su ka yaudarar da sarakai ta kamu da ciwon son sa ta dinga zuwa har cikin firsuna ta na taimakonsa tare da shan alwashin sai ta fitar da shi daga halin kuncin da ya ke ciki.
Usman na da shekaru bakwai a ka fara shigar da shi daji a na gogar da shi ilimin yaki tun daga kan fada da mutane har zuwa dabbobi tare da koya masa dabarun fada da takobi da mashi da iya harbi da kwari da baka da sauransu.
Ya na da shekaru goma sha biyu ya kware sosai ya zama sadauki a fagen yaki duk kasar yammawa an sallama masa har su na yi masa kirari a shafi na 12 su na cewa ” Usman Mai duniya na Kaura yalli, gwaggon biri makashin maza”.
A lokacin ne a ka sanar da Usman labarin mahaifinsa da irin wulakancin da Damangawa su ka yiwa masarautarsa.
Ai kuwa Usman Mai duniya ya shirya tare da abokinsa Sabi’u wanda su ka taso tare dan Kaura yalli wato kawun Usmankenan, su ka nausa daji.
Shi kuwa Sarki Haruna Kabir Zubaida ta kubutar da shi daga gidan kurkukun sun shiga duniya, in da suka yi aure daga bisani wahalar da ya sha a kurkuku ta kwantar da shi ciwo.
Jarumta
Usman kuwa tun shigarsu daji ya ke nuna jarumtarsa in da ya kashe Gada suka cinye a shafi na 23, sannan ya gwabza yaki da wasu ‘yan rawar wuta a shafi na 26, ya yi gumurzu da Sarkin fawa a shafi na 27. Sun buga gumurzu da mayakan garin Dawaki a shafi na 32 in da su ka biyo bayansu, maimakon Usman ya gudu sai su ka tsaya suna cafe mashi da kibbau, in da ya ke yi wa kansa kirari, “Kai arna ba ku sanni ba ne? Ni ne Usman Mai duniya, gwaggon biri makashin maza ni ne hadari malfar duniya”. Nan ya afka musu ya karkashe su.
Haduwarsu da aljani wanda ya ba Usman takobin kakansa da suka ara su kai yaki a shafi na 33-34.
Usman ya shiga gasa a kasar Zainawa in da ya yi dauki ba dadi da mayaka abokan takara a shafi na 36.
Sannan ya gwabza da sarkin yakin garin Kaura Malle wanda manyan baraden nahiyar ke shakkar arangama da shi saboda rashin tausayinsa, amma Usman bai saurara ba sai da ya fatattaka jikin Kaura Malle ya cinye gasar a shafi na 37-39.
Ya taimakawa Sarkin Zainawa sun yaki mutanen kasar Dawaki in da ya gwabza da manyan mazaje da kauraye a shafi na 55 sannan ya yi gumurzu da Sarkin in da ya shafe shi a doron kasa……..

But none of them need new pay someone to do homework legislation to hang onto their waivers

%d bloggers like this: