SADAUKI MAI DUNIYA – 3

Matan nan su kai nasarar mamaye gidajen sarakan Kwairanga in da a karshe su ka kare musu kallon sirri a ranar wani biki na al’ada da Kwairanga ke gudanarwa duk shekara a ka turo maza mayaka daga Damanga, ‘ yanmata sukashayar da sarakai giyasu bayan sun sha sun bugu su ka hadu su ka cinyesu da yaki da rana tsaka, su ka karkashe mutane su ka nufi fada wajen Sarki, in da ya nuna jarumtarsa a shafi na 9 ‘ Maharan Damanga su ka yi ca kan Sarki Haruna, shi kuwa gogan naka ko in kula sai faman kirari ya ke yana cewa “Sai ni dan mutan Kwairanga kadangaren bakin tulu, a kar ka a kar tulu a bar ka ka bata ruwa, ruwan dare dama duniya na kwairanga sai dubu ta taru, ai kuwa nan da nan suka taru a kansa su ka kame Sarki Haruna Kabir su ka tafi da shi garinsu su ka daure, cikin matansa kuwa akwai wata da a ke kira Hassana wacce ta haye doki ta kubuta ta gudu tare da goyon danta Usman, ‘yar Wani sarki sadauki jarumin gaske ne a wata kasa da a ke kira Yammaniya. Bayan ta sanar da mahaifinta yadda a ka tarwatsa kasar maigidanta Sarki Haruna, sai ya jajanta lamarin kuma ya dauki aniyar horar da Usmanu don ya daukarwa mahaifinsa fansar abinda a ka yi masa.
Sarki Haruna kuwa ya na daure a can wani kurkukun karkashin kasa a kasar Damanga in da ya shafe shekaru cikin wahala da azabtarwa iri-iri, yayin da kuma Zubaida daya daga cikin matan da a ka tura Kwairanga su ka yaudarar da sarakai ta kamu da ciwon son sa ta dinga zuwa har cikin firsuna ta na taimakonsa tare da shan alwashin sai ta fitar da shi daga halin kuncin da ya ke ciki.
Usman na da shekaru bakwai a ka fara shigar da shi daji a na gogar da shi ilimin yaki tun daga kan fada da mutane har zuwa dabbobi tare da koya masa dabarun fada da takobi da mashi da iya harbi da kwari da baka da sauransu.
Ya na da shekaru goma sha biyu ya kware sosai ya zama sadauki a fagen yaki duk kasar yammawa an sallama masa har su na yi masa kirari a shafi na 12 su na cewa ” Usman Mai duniya na Kaura yalli, gwaggon biri makashin maza”.
A lokacin ne a ka sanar da Usman labarin mahaifinsa da irin wulakancin da Damangawa su ka yiwa masarautarsa.
Ai kuwa Usman Mai duniya ya shirya tare da abokinsa Sabi’u wanda su ka taso tare dan Kaura yalli wato kawun Usmankenan, su ka nausa daji.
Shi kuwa Sarki Haruna Kabir Zubaida ta kubutar da shi daga gidan kurkukun sun shiga duniya, in da suka yi aure daga bisani wahalar da ya sha a kurkuku ta kwantar da shi ciwo.
Jarumta
Usman kuwa tun shigarsu daji ya ke nuna jarumtarsa in da ya kashe Gada suka cinye a shafi na 23, sannan ya gwabza yaki da wasu ‘yan rawar wuta a shafi na 26, ya yi gumurzu da Sarkin fawa a shafi na 27. Sun buga gumurzu da mayakan garin Dawaki a shafi na 32 in da su ka biyo bayansu, maimakon Usman ya gudu sai su ka tsaya suna cafe mashi da kibbau, in da ya ke yi wa kansa kirari, “Kai arna ba ku sanni ba ne? Ni ne Usman Mai duniya, gwaggon biri makashin maza ni ne hadari malfar duniya”. Nan ya afka musu ya karkashe su.
Haduwarsu da aljani wanda ya ba Usman takobin kakansa da suka ara su kai yaki a shafi na 33-34.
Usman ya shiga gasa a kasar Zainawa in da ya yi dauki ba dadi da mayaka abokan takara a shafi na 36.
Sannan ya gwabza da sarkin yakin garin Kaura Malle wanda manyan baraden nahiyar ke shakkar arangama da shi saboda rashin tausayinsa, amma Usman bai saurara ba sai da ya fatattaka jikin Kaura Malle ya cinye gasar a shafi na 37-39.
Ya taimakawa Sarkin Zainawa sun yaki mutanen kasar Dawaki in da ya gwabza da manyan mazaje da kauraye a shafi na 55 sannan ya yi gumurzu da Sarkin Dawakin in da ya gwada masa cewa jarumta fa ba a karami take ba kuma ba a babba ta ke ba, a wajen mai zuciya ta ke.
Usman da Sabi’u sun gwabza gumurzun yaki da mayakan kasar Damanga a Kasar Dadin kowa a shafi na 88/90.
Sun sake kutsawa yaki kasar Kwairanga daukar fansa domin bayan ture Sarki Haruna Kabir sai Sarki Sakimu ya dora kaninsa Mantau a gadon sarautar kasar, a shafi na 101/103, su Usman Mai duniya da Sabi’u sun kawar da Sarki Mantau yayin da Sarki Haruna ya koma kan gadon Sarautarsa da Damagawa su ka tsige shi.
Jarumtar kwarai mai nuna bajinta da ban sha’awa ta mayakan hadin gwiwan kasar Dadin kowa da Zainawa da Kwairanga da kuma Kaura Yalli na kasar yammaniya ta yi arangama da rundunar mayakan Kasar Damanga domin daukar fansa a kan Sarki Sakimu wanda ya addabi yankin a shafi na 105/110 wannan gumurzu shi ne ma fi hatsarin gaske da sarakunan su ka yi. Mata ma ayarin gimbiya Sailuba sun buga gumurzu karkashin Batulu in da su ka karkashe mazajen Damanga.
Usman ya yi arangama da Sarki Sakimu in da su ka yi ta dauki ba dadi ga juna har dai Usman ya sassare masa hannuwa biyu tun daga kafada duk da ganin an kassara Sakimu Zakin Hamada mayakansa ba su saduda sun gwada tsabar taurin kai da masifa sai da Usman mai duniya ya shayar da su ruwan kokon mutuwa, jini ya dinga kwarara, hannuwa da kafafuwa iri-iri kawuna kuwa ba adadi sannan ‘yan tsirarun Damangawa su ka sallama, a ka ja Sarki Sakimu zuwa kasarsa ta Damanga gaban talakawansa da ya ke yiwa zalunci ya ke kashewa da izza a ka kashe shi, a ka ba talakawa zabi su ka zabo wanda su ke so a ka nada musu.
Soyayya,
Sarki Haruna ya yi soyayya da Zubaida a shafi na11/12, 21/24 wacce soyayya ce mai cike da tausayi tare da nunawa juna kauna In da a karshe su ka yi aure.
Usman mai duniya da Gimbiya Sailuba ‘yar sarkin Zainawa a shafi na 40/42, 47/48
Soyayya ce ta sadaukarwa da nuna tarairayar juna.
Sabi’u ya yi soyayya ta hakika da Safara’u ‘yar hakimin Dawaki a shafi na 27/29 in da ya yi takara da dan Galadiman garin.
Usman ya yi soyayya da Aisha a kasar Dawaki.
Littafin ya cika burin taurarin na daukar fansa tare da kai su karagar sarauta da kuma auren matayen da su ke so.
Bugu
Babu laifi a bisa bugun littafin da kuma wallafuwarsa a dunkulallen littafi guda daya da kasantuwarsa mai sahihiyar lambar bugu ISBN.
Tsarin shafuka ya tsaru.
Zanen bango ya dakko hoton ainahin gumurzun da ke cikin labarin.
Kura-kurai
An ce komin iyawarka da kallo mai kallon ka ya fi ganinka, duk irin kokarin da a ka yi wajen kiyaye dokoki da ka’idodin rubutu an dan samu hadewar wasu kalmomi da ya dace a rarrabasu a shafi na 4 koina maimakon ko’ina
a shafi na 5 suka maimakon su ka.
Irin wadannan kananan kura- kurai dai a kan same su tsilla-tsilla cikin littafin.

%d bloggers like this: